Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsaro: An Yi Taron Majalisar Koli Ta Tsaron Najeriya


Shugaba Buhari
Shugaba Buhari

A cigaba da lalubo mafita game da matsalolin tsaro da rayuwa a Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki, inda ya ciza ya kuma hura.

An Yi Taron Majalisar Tsaron Kasa Karkashin Shugaba Buhari

Bayan baban kalubalen tsaro da na zamantakewa da Najeriya ta fuskanta wanda ya kuma dada dagulewa sanadiyyar zanga zangar ENDSARS ta kwanan nan, Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya jagoranci wani taro na majalisar Tsaron Kasa don tattaunawa kan abubuwan da su ka gabata, da wadanda su ka faru a lokacin da kuma wadanda su ka biyo baya don maganin nan gaba.

Wannan taro na kwamitin koli kan tsaro, ya samu halartar mambobin majalisar sojoji ta Najeriya da Ministan Tsaro da kuma na Ayyukan ‘Yan Sanda masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro da kuma sauran wadanda abin ya shafa, da zummar gano bakin zaren.

Ministan ‘yan sandan Najeriya, Alhaji Muhammadu Dingyadi, ya ce a wannan ganawar Shugaban Najeriya ya yi alkawarin cewa za a cigaba da sauraron duk wadanda ya kamata a saurare su saboda a samu warware matsalolin. Y ace za a cigaba da tafiya da matasa da sauran mutane da magabata kuma za a tabbatar cewa duk wasu masu hakki an ba su saboda a zauna lafiy

Nigerian soldiers march during 58th anniversary celebrations of Nigerian independence, in Abuja, Nigeria, Monday, Oct. 1, 2018. (AP Photo/Olamikan Gbemiga)
Nigerian soldiers march during 58th anniversary celebrations of Nigerian independence, in Abuja, Nigeria, Monday, Oct. 1, 2018. (AP Photo/Olamikan Gbemiga)

To saidai Ministan y ace gwamnati ba za ta zura ido wasu mutane tsiraru su yi ta aika aika har al’amarin ya kai ga nakasa gwamnati. Ya yi kira ga jama’a da su bada gwamnati cikakken goyon baya kuma a bai wa gwamnati sarari na sauraron bukatun gwamanti. Y ace dokar Najeriya ba ta ce a murkushe zanga zanga ba; ta ce ne a tattauna da jama’a.

Alhaji Dingyadi y ace taron ya kuma tabo batun matsalar tsaro a hanyar Abuja zuwa Kaduna. Ya ce miyagun dajin sun sace wasu mutane to amma an yi nasarar sake kwato wasu.

Ga Umar Faruk Musa da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00


Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG