Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsaro: Karamar Hukumar Ungogo A Kano Ta Kaddamar Da Cibiyar Yi wa Jama’ar Yankin Rijista


Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke umartar gwamnonin kasar su hada hannu da masu rike da sarautu da shugabannin kananan hukumomi domin tabbatar da tsaro a yankunansu, karamar hukumar Ungogo a jihar Kano ta kaddamar da cibiyar yi wa Jama’ar yankin rijista.

Yin rijistar, zai ba mazauna yankin damar samun wani katin shaida a wani mataki na tabbatar da tsaro.

Cibiyar wadda aka samar da kayayyakin sadarwa na zamani a cikin ta, za ta rinka tattarawa, da adana bayanai da kuma bada katin shaida ga duk dan asalin yankin na Ungogo.

Abdullahi Garba Ramat dake zaman shugaban karamar hukumar ta Ungogo ya ce batun tsaro na daga dalilan samar da wannan cibiya.

Ko da yake, galibin mazauna yankin na Ungogo na da karancin masaniya game da wannan sabon tsari, amma ga alama sun yi maraba da shi.

Tuni dai hukumar NITDA mai bunkasa harkokin fasahar sadarwa a Najeriya ta bayyana aniyar tallafawa wannan tsari, in ji Shiekh Lawan Abubakar da ke zaman mai tsare-tsarea shiyyar arewa maso yammacin Najeriya na hukumar.

Karamar hukumar Ungogo dai na cikin kananan hukumomi 8 na kwaryar birni da kewayen Kano kuma wasu sassa na manyan hukumomin gwamnatin tarayya, kamar filin jirgin sama na Kano da Jami’ar Bayero na cikin yankunanta.

Saurari cikakken rahoton a ciki sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG