Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Dan Wasan Kwallon Kafa Na Amurka, Aaron Hernandez Ya Rataye Kansa


An tsinci tsohon dan wasan kwallon kafar Amurka, Aaron Hernandez a mace a cikin dakinsa na gidan yari dake jihar Massachusetts a nan Amurka.

Hukumomi sun ce dan wasan mai shekaru 27, wanda ya taba bugawa kungiyar New England Patriot wasa, ya rataye kansa ne ta hanyar amfani da abin shimfidar gadonsa wanda ya kulla a jikin taga ko kuma wando ya rataye kansa.

Baya ga haka, Hernandez ya kuma yi yunkurin datse kofar shiga dakin na sa daga ciki, inda ya saka abubuwa da dama domin ya tokare ta, in ji wani jami’in gidan yarin mai suna Christopher Fallon.

Rahotanni sun ce an kebe Hernandez ne a wani daki daban a cikin babban gidan yarin na jihar ta Massachusetts.

Bayan an same shi a kwance ne sai aka garzaya da shi zuwa asibti, amma aka tabbatar cewa ya mutu yayin d aka isa.

Shi dai Hernandez ya na zaman gidan yari ne bayan da aka yanke mai hukuncin daurin rai da rai inda aka same shi da laifin kisan kai a shekarar 2013, koda ya ke an wanke shi a baya.

Shi dai Hernandez ya buga wa kungiyar sa ta New England Patriots a kakar wasanni uku a gasar NFL ta Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG