Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Ya Sami Sabon Mukami A Uganda


Yarin bikin nadin mukimin a Uganda.
Yarin bikin nadin mukimin a Uganda.

An nada tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan a matsayin shugaban Jami’ar Cavendish ta kasar Uganda a hukumance.

Jami'ar Cavendish ta dora Jonathan a matsayin ‘Chancellor’ a wani gagarumin bikin ranar Alhamis da yamma.

Jami’ar ta Cavendish wadda ba ta gwamnati ba ce, tana daya daga cikin manyan jami’o’i a nahiyar Afirka.

An bude jami’ar ne a shekarar 2008, inda ta soma gudanar da ayukan ta a karkashin shugabancin tsohon shugaban kasar Zambia, marigayi Kenneth Kaunda, wanda ke matsayin ‘Chancellor’ na jami’ar.

Nadin ya sa Jonathan ya zama shugaban jami’ar na uku tun kafuwar ta.

Marigayi Kenneth Kaunda, tsohon shugaban Jamhuriyar Zambiya, shi ne shugabar gwamnatin farko, da Benjamin Mkapa, marigayi shugaban Jamhuriyar Tarayyar Tanzania, kansila ta biyu.

Ga abin da tsohon shugaban ke cewa a shafinsa na Facebook:

“Na yi farin ciki da aka ƙaddamar da ni a hukumance a matsayin Shugaban Jami'ar Cavendish ta Uganda kuma na yi aikina na farko a hukumance a wannan matsayin a bikin yaye dalibai na 10 na Jami'ar a yau a Kampala, Uganda.

Ina taya sabbin wadanda suka kammala karatu murna da rokon su da su tabbatar da tasirin ilimin su zuwa ga mutane, da kuma gina al'ummar masu kawo sauyi da inganta al'umma”.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG