Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tun Ina 'Yar Shekara 7 Mahaifina Yake Lalata Da Ni - Yarinya 'Yar Shekara 12


'Yan mata.

Rudunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wani mutum mai shekaru 49, bisa zargin yi wa ‘yar sa mai shekaru 12 da haihuwa fyade.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ogun da ke kudancin Najeriya, DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar, ta ce an kama mutumin mai suna Ubong Williams Akpan, bayan da ‘yar tashi ta kai karar sa a ofishin ‘yan sanda da ke Itele Ota a jihar ta Ogun.

A cewar DSP Oyeyemi, yarinyar ta ce tun tana ‘yar shekara 7 ne mahaifin nata yake kwanciya da ita da kuma cin zarafinta.

Yarinyar ta kara da cewa ta kai kara a ofishin ‘yan sandan ne bayan da mahaifin na ta ya kwashe tsawon shekara 5 yana tursasa yin lalata da ita, kuma a yanzu ta gaji da wannan al’amarin.

Karin bayani akan: auren yara, jihar Ogun, Nigeria, da Najeriya.

Bayan kai karar ne, DPO na ofishin ‘yan sandan na Itele Ota, CSP Monday Unoegbe ya shirya runduna, wadda ta yi bincike tare ka kamo wanda ake zargin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan ta jihar Ogun ya ce wanda ake zargi ya amsa cewa ya aikata laifin da ake tuhumarsa, inda ya ce yanayin matarsa ne ya jefa shi a cikin wannan halin.

Wanda ake tuhumar ya ci gaba da fadawa ‘yan sanda cewa “matarsa ta tsufa, kuma ba ta ba shi sha’awa.”

Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Ogum Edward Awolowo Ajogun
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Ogum Edward Awolowo Ajogun

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Ogun, Edward Awolowo Ajogun, ya ba da umarnin a mika lamarin ga sashen kula da lamurran iyali na ofishin yankin Ota na rundunar ‘yan sanda, domin ci gaba da bincike, da kuma gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.

Haka kuma ya ba da umarnin kai yarinyar a babbar asibiti, domin kula da duba lafiyarta.

XS
SM
MD
LG