Accessibility links

Matsalolin Tsaron Dake Addabar Kasashen Afirka Su Na Da Yawa In Ji Janar Dambazau


Wani dan sanda yana duba gine gine da ababan hawa da kuma makamai bayan harin da kungiyar Boko Haram ta kai a Damaturu ranar 25 da 25 ga watan Oktoba. An dauki hotunan ranar 28 ga watan Oktoba, 2013.

Rashin tsaron bakin iyakoki shi ne babban abinda ke haddasa fitina domin ta nan ake satar shiga da makamai da wasunsu in ji tsohon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya

Matsalolin tsaron da suke addabar kasashen Afirka, sun zarce batun ta'addanci kawai, domin sun hada har da dillalan muggan kwayoyi dake amfani da nahiyar a zaman zango wajen safarar kwayoyinsu, da safarar makamai, sai kuma uwa uba batun rashin shugabanci.

Tsohon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Abdurrahman Bello Dambazau, shi ne ya bayyana wannan a lokacin da yake hira da Muryar Amurka.

Janar Dambazau yace rashin shugabanci na kwarai a kasashenmu na Afirka, na haddasa cin hanci da rashawa, da kawo koma bayan tattalin arziki, da lalata harkar ilmi da kyautata jin dadin al'umma, abubuwan da su kan taru su kara wutar tashin hankali.

Game da batun rashin tsaro, musamman a yankin arewacin Najeriya, Janar Dambazau yace tilas sai an samu hadin kan kasashe makwabtan Najeriya domin kuwa ta cikin wadannan kasashe makwabta ake shigo da makaman da 'yan ta'adda da 'yan fashi ke amfani da su.

Janar din yayi misali da cewa tsawon bakin iyakar Najeriya da kasashe kamar Kamaru da Chadi da Nijar ya kai dubban kilomitoci, amma kuma tasoshin bakin iyaka guda 57 tak Najeriya take da su. Alhali kuma akwai barayin hanyoyi fiye da dubu daya da dari biyar wadanda ake amfani da su wajen shiga da fita daga kasar.

XS
SM
MD
LG