Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ukraine Na Bukatar Tallafin Gaggawa - Blinken

 Antony Blinken
Antony Blinken

Kalaman na Blinken na zuwa ne biyo bayan ganawar da ya yi da ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar tsaro ta NATO a lokacin da ake dada samun damuwa kan yiwuwar cewa Rasha tana karfafa mataken (makaman) kariyar ta da tallafi daga China, Koriya ta Arewa da Iran.

Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya fada a ranar Alhamis cewa akwai bukatar bai wa Ukraine karin tallafi cikin gaggawa.

Kalaman na Blinken na zuwa ne biyo bayan ganawar da ya yi da ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar tsaro ta NATO a lokacin da ake dada samun damuwa kan yiwuwar cewa Rasha tana karfafa mataken (makaman) kariyar ta da tallafi daga China, Koriya ta Arewa da Iran.

“Daga bayanan da na samu yau, kowace kasa har da Amurka za ta kara azama, sannan akwai bukatar kara kaimi wajen nemo yadda za a samarwa Ukraine kayayakin da ta ke ci gaba da bukatar su” abin da Blinken ya fadawa manema labarai kenan bayan kamala ganawar da ya yi da ministocin harkokin wajen kasashen kawancen NATO a shalkwatar kungiyar da ke Brussels.

UKRAINE-CRISIS/ATTACK-KHARKIV
UKRAINE-CRISIS/ATTACK-KHARKIV

Yayin da mambobin NATO a radin kansu suke baiwa Ukraine tallafin makamai, kungiyar a matsayin tsintsiya ta mai da hankali akan samar mata da tallafin makamai da ba sa kisa domin kaucewa ta’azarar tashin hankali da Rasha akan gudunmawar su kai tsaye.

"Ya zuwa yanzu, sama da kasashe 30 sun kulla ko suna kokarin kulla alaka tsakaninsu da Ukraine, mu kan mu Amurka, muna kokarin kulla tamu alakar da ita", ya sheda.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG