Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Venezuela Ta Saki Wasu Amurkawa Biyu


Joshua Holt da mai dakinsa

Kasar Venezuela ta saki wasu Amurkawa biyu da ta tsare a matsayin fursunoni tun a shekarar 2016, bayan da ta tuhume su da laifin boye makamai a kasar.

Wani Ba’amurke da aka tsare shi a matsayin fursuna a Venezuela tun a shekarar 2016, ya koma kasarsa.

Joshua Holt da mai dakinsa, Thamy Candelo, sun iso Amurkan tare da rakiyar Sanata Bob Corker, wanda ya shiga tsakani aka sake su.

Holt da matarsa sun kwashe shekaru biyu a tsare a kasar ta Venezuela, tun bayan da aka tuhume su da laifin boye makamai.

A ranar Juma’a, Corker ya gana da shugaban Venezuela, Nicolas Maduro.

Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, “ina mai matukar farin ciki, Josh Holt ya komo gida tare da iyalinsa, za a ci gaba da barin takunkumi a kan Venezuelan har sai ta koma kan turbar Dimokradiyya.”

A daren jiya Asabar, Holt da sauran jami’an gwamnatin Amurka, suka gana da shugaba Donald Trump a fadarsa ta White House.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG