Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Venezuela:Ana Fatautar Wadanda Suka Kai Harin a Sansanin Soji


Nicolas Maduro

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya fada jiya lahadi cewa, dakarunsa sun murkushe wani hari da aka kai na dan karamin lokaci kan sansanin soji, karkashin jagorancin wani tsohon jami’in soja da ya bijire.

Maduro ya bayyana harin a matsayin aikin ta’addanci da Amurka da kuma Colombia suka dauki nauyi, sai dai bai bada shaidar harsashen nasa ba a jawabinsa na Lahadi lahadi da ake yayatawa a talabijin.

A kalla mutane biyu aka kashe daga cikin maharani lokacin da aka yi musayar wuta jiya lahadi da asuba, inda dakarun sujin suka sha karfin ‘yan tawayen a sansanin dake kusa da birnin Valencia, dake tsakiyar Venezuela.

Bayanan Maduro da na jami’an kasar Venezuela na nuni da cewa, kimanin mutane ishirin suka kai harin a sansanin sojin.

Goma daga cikinsu, sun arce kafin dakarun Venezuela su isa wurin, yayinda wadanda aka bari a baya suka yi musayar wuta da sojojin har zuwa kimanin karfe takwas na safe kafin aka kashe su duka ko kuma aka kamasu

Maduro yace, an kan farautar wadanda suka arce.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG