Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Adawa A Zimbabwe Ya Shiga Hannun 'Yan Sanda


Dan Sandan Zimbabwe
Dan Sandan Zimbabwe

An kama wani dan adawan Zimbabwe Tendai Biti a kan iyakar kasar da Zambia.

Lauyan Biti, Ngobizitha Mlilo yace an kama Biti ne yayin da yake kokarin tsallaka iyaka zuwa Zambia domin neman mafakar siyasa.

Biti yana cikin mambobin jami’iyar adawa ta Movement for Democratic Change alliance (MDC) da 'yan sandan Zimbabwe ke farautarsu saboda iza tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa da aka yi a makon da ya gabata, wanda MDC alliance take zargin an tabka magudi a ciki, da ya baiwa shugaba Emmerson Mnangagwa daman lashe zaben.

Biti ya yi taron manema labarai wuni guda kafin ayyana shugaba Mnangagwa wanda ya lashe zabe, yana mai cewar dan takarar MDC Nelson Chamisa ne ya lashe zaben na ranar 30 ga watan Yuli.

Washe gari, da magoya bayan Chamisa suka gudanar da zanga zangar kalubalantar sakamakon zaben, 'yan sanda kuma mai da martani mai gautsi, inda suka yi amfani da barkonon tsuhuwa da harsashai a kan masu zanga zangar, kana suka kashe mutane shida

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG