Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Birtaniya Ya Cika Burinsa Na Kure Tsawon Afirka kilomita 10,000 Da Gudu A Cikin Kwanaki 352


Russ Cook
Russ Cook

A ranar Lahadin da ta gabata ne dan tsere Russ Cook ya isa yankin arewacin Afirka, kusan shekara guda bayan ya tashi daga kudancin nahiyar a yunkurinsa na kure tsawon nahiyar da gudu.

Magoya bayansa da dama sun taru a wani shingen dutse da ke gefen tekun Meditareniya a arewacin Tunisiya, inda suka yi ta jinjina ma dan tseren, wanda ya yi gudun tsawon kilomita sama da 16,000 a cikin kasashe 16 cikin kwanaki 352.

Yayin tafiyarsa dan tseren nuna juriyan mai shekaru 27, wanda ya fito daga Worthing a kudancin Ingila, ya tsallaka dazuzzuka da hamada, ya kuma zagaye wuraren da ake rikici yayin da kuma ya samu jinkiri saboda sata, rauni da matsalolin biza.

Tunisia Running Across Africa
Tunisia Running Across Africa

Cook - wanda a kafafen sada zumunta ake wa lakabi da Hardest Geezer - ya tashi ne a ranar 22 ga Afrilun, 2023 daga Cape Agulhas a Afirka ta Kudu, yankin kudu maso yammacin nahiyar da niyyar ya kammala gudun cikin kwanaki 240.

Sai dai wasu ‘yan fashi da makamai sun sace wa shi da tawagarsa kudi, fasfo da kayan aiki a Angola. Haka kuma ciwon baya ya dakatar da shi na wani dan lokaci a Najeriya.

Britain's Russ Cook becomes the first person to run the entire length of Africa
Britain's Russ Cook becomes the first person to run the entire length of Africa

Cook, a baya ya yi gudun kilomita 3,000 (mil 2,000) daga Istanbul zuwa Worthing a cikin kwanaki 68.

"Tafiyar kwanaki 352 kan hanya na dogon lokaci ba tare da ganin dangi ba na da matukar wahala. Jikina ya mani ciwo sosai. Amma sauran ma ni rana guda, don haka bazan yi korafi ba.” A cewar Cook ga Sky News.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG