Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani dan kunar bakin waken Taliban ya hallaka sojojin Afghanistan


Mayakan Taliban

Wani dan kunar bakin waken kungiyar Taliban ya hallaka sojojin Afghanistan su akalla 3 yau litinin, tare da raunata wasu su 18 a lardin Balkh na arewacin kasar.

Jami’an Afghanistan, sun bayyana cewa an auna kai harin ne kan wata mota kirar Bus dauke da jami’an rundunar sojan kasar da ake kira ANA a takaice, a gundumar Dahdadi. Shaidun gani da ido, sun fadawa manema labarai cewa sun ga akalla mutane 8 da su ka mutu. Rahotanni kuma sun ce akwai mata 3 da ke aiki a rundunar sojojin lardin cikin wadanda su ka jikkata.

Mai magana da yawun ‘yan kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid, a wata sanarwa ga manema labarai, ya ce ‘yan kungiyar ne su ka kai harin, kuma ya ce wadanda su ka mutu na da yawa. Zabihullah ya fadi cewa maharin ya shiga motar ne kafin sojojin su shiga zuwa wajen aikinsu inda ya tada bom din.

‘Yan sa’o’I bayan harin, jami’ai daga lardin Paktika da ke kusa da iyakar Pakistan a gabashin kasar, sun ce ana zaton wani harin kunar bakin wake a wata kasuwa cike da jama’a ya kashe akalla farar hula 6 da raunata wasu su 9. kafafen yada labaran Afghanistan sun ce ga dukan alamu maharin ya auna ‘yansanda da ‘yan leken asiri ne a lokacin da suke cin abinci a gundumar Yahyakhel.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG