Accessibility links

Wani Kamfani Mai Zaman Kansa Zai Samar da Wutar Lantarki a Jihar Borno

  • Ibrahim Garba

Faya fayen tarar karfin wutar lantarki daga hasken rana

Attajirin nan da ke jihar Borno mai suna Mohammed Indimi ya sha alwashin kafa wani katafaren kamfanin samar da wutar lantarki a jihar Borno don kawo karshen durkushewar masana'antu sanadiyyar rashin wutar lantarki

A wani yinkuri na kawo karshen fama da rashin wutar lantarkin a jihar Borno, hamshakin dan kasuwannan da ke jihar, Alhaji Muhammad Indimi ya yi alkawarin kafa wani babban kamfanin wutar lantarki mai suna Oriental Energy Resources da zai samar da wutar lantarki ga jama'a da masana'antu a jihar don a yi walwala, kamfanoni su bunkasa matasa da sauran jama'a su sami ayyukan yi.

Wakilinmu na jihar Borno da ya aiko mana wannan rahoton, Haruna Dauda ya ce hatta tashe-tahsen hankulan da ake fama da su ana danganta su da rashin ayyukan yi sanadiyyar durkushewar masana'antu sanadiyyar rashin wutar lantarki. Hasalima, in ji Haruna, gwamnati ta sha ware makudan kudade da zummar inganta bangaren wutar lantarki na kasa baki daya amma an kasa gani a kasa.

Haruna ya ruwaito hamshakin dan kasuwan na cewa kamfanin samar da wutar lantarkin da zai kafa din mai amfani ne da hasken rana wajen samar da wutar lantarkin, wanda ake kira Solar Energy. Ya ce muddun kamfanin ya fara aiki zai samar da wuta ga dukkan kananan hukumomin 27 da ke cikin jihar. Alhaji Indimi ya ce lallai lokaci ya yi da su 'yan kasuwa za su taka tasu rawar wajen samar da wutar lantarki a Nijeriya.

XS
SM
MD
LG