Accessibility links

Za a Yi Babban Taron Tattalin Arzikin Arewa Maso Gabas a Gombe

  • Ibrahim Garba

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi.

A wani yinkuri na farfado da tattalin arzikin arewa maso gabashin Nijeriya da ke tangal-tangal, za a yi wani babban taron tallata wuraren saka jari da ke jihohi shida na yankin a garin Gombe ranar Talata.

Manyan 'yan kasuwa daga China da Australia da Ukraine da sauran kasashe ne ake sa ran za su bi sahun takwarorinsu na Nijeriya wajen halartar wani babban taro kan cinakayya da tattalin arziki da za a yi a birnin Gombe, hedikwatar jihar Gombe jibi Talata.

Da ya ke bayani ga wakiliyarmu Saadatu Mohammed Fawu, Shugaban kwamitin shirya taron Shugaban Kwamitin shirya taron Alhaji Mohammed Kabir Ahmed ya ce za a nuna ma masu halartar taron dinbin wuraren saka jarin da ke akwai a jihohin arewa maso gabashin Nijeriya.

Ya kuma gaya ma wakiliyarmu cewa za a sa ido sosai a tabbatar cewa an yi anfani da shawarar da aka cimma wurin taron. Hasalima, in ji shi, za a kafa kwamitin tabbatar da cewa an aiwatar da abubuwan da kwararru su ka bayyana aka kuma tabbatar da su saboda cigaban yankin na arewa maso gabashin Nijeriya.

XS
SM
MD
LG