Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Kwamitin MDD Yayi Allah Wadai Da Mamayar Da Rasha Ta Yiwa Crimea


Shugaban Rasha Vladimir Putin

Wani kwamitin Majalisar dinkin duniya jiya Talata ya amince da wani daftari da a ciki aka yi Allah wadai da mamayar da Rasha ta yiwa yankin Crimea, kudurin ya sake nanata cewa bai amince da kamawa da hade yankin na Crimea da Rasha da Moscow tayi.

Daftarin ya sami amincewar wakilai 73, 23 suka ki amincewa, 76 suka kaurace. Ana kyautata zaton daftarin zai sami amincewar dokacin babban zauren MDD a zamanta cikin watan gobe.

Kudurin ya yi kira ga Rasha ta mutunta hakkokinta na kasa da kasa a matsayin wacce tayi mamaye, sannna ta dauki duk wasu matakai da suka kamata domin gaggauta kawo karshen muzgunawa mazaunan Cremia, sannna da gaggauta sakin wadanda aka tsare bada laifiba. Kana su tabbatarda babu wani tsaiko wajen bada dama ga masu kula da hakkkokin Bil'adama da kuma ma’aikata.

A wani bangaren kuma Shugaban Rasha Vladmir Putin, ya yanke hukuncin kasarsa ta fice daga babbar kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuffuka.

Putin ya rattaba hannu akan dokar a yau Laraba wacce ta cire Kasar daga kotun kasa da kasa irnta ta farko wacce take da hurumi na sai illa masha'allahu na hukunta laifuffukan kisan kare dangi, cin zarafin Bil'Adama da kuma laifuffukan da aka aikata a fagen yaki.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG