Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Sojan Kiyaye Zaman Lafiya Na Majalisar Dinkin Duniya dake Mali Ya Rasa Ransa


Mayakan Tuareg dake kaiwa sojojin MDD hari a Mali

Wani sojan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice, ya rasa ransa, wasu da dama kuma sun jikkata a arewa maso gabashin Mali, bayan da wani hari makamancin na roka ya afkawa sansaninsukusa da iyakar kasar Algeria.

A wata sanarwa da ta bayar, MDD ta fadi cewa an kaiwa wasu gine-ginen ta guda 4 a Aguelhok hari a lokuta dabam-dabam jiya Litinin, abinda yayi sanadiyyar mutuwar wani sojan wanzar da zaman lafiya daga kasar Chadi tare da raunata wasu su 8.

Sakatare-Janar na MDD Ban Ki-moon yayi kira akan a dauki matakai cikin gagawa akan wadanda ke da alhakin kai wadannan hare-haren, wanda yace sun isa zama laifukan yaki bisa dokar kasa-da-kasa.

Har yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.

A shekarar 2012 masu ikirarin su yan Jihadi ne suka mamaye bangaren da aka kai harin a arewacin Mali. Matakin soja da dakarun Faransa suka dauka a shekarar 2013 ya fatattaki mayakan sa-kan daga makeken yankin dake a arewacin Mali, amma duk da haka har wayau suna ci gaba da rike wasu sassa ayankin.

Har yanzu kungiyoyin da ke da alaka da al-Qaida na kai hare-hare a yankin, kuma zuwa yanzu a cikin shekarar nan an kashe sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD guda 32 a Mali.

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG