Accessibility links

Wasu Kasashen Afirka Suna Renon Likitoci, Amma Kasashen Yamma Ne Suke Amfana

  • Aliyu Imam

Likita yake auna wani yaro a birnin Harare.

Wani bincke da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya a Ingila, yace kasashen Afirka dake kudu da Hamadan sahara, wadanda suka kashe kudi wajen horas da likitoci sun yi hasarar dubban miliyoyin dala, ganin masu aikin lafiyar suna barin kasashen.

Wani bincke da aka wallafa a mujallar kiwon lafiya a Ingila, yace kasashen Afirka dake kudu da Hamadan sahara, wadanda suka kashe kudi wajen horas da likitoci sun yi hasarar dubban miliyoyin dala, ganin masu aikin lafiyar suna barin kasashen zuwa kasashe da suka ci gaba, domin neman aiki.

Wadanda suka gudanar da binciken da aka wallafa a mujallar likitocin suka ce kasashe tara da suka gudanar da wan nan bincike akansu, sune Ethiopia, Kenya, Malawi, Nigeria, da Afirka ta kudu, da Tanzania, da Uganda, Zambia, da kuma Zimbabwe, sun yi hasarar akalla dala milyan dubu biyu a horasda likitoci wadan da daga bisani suka kaura zuwa kasashen waje. Rahoton yace Afirka ta kudu da Zimbabwe su suka fi nakasa.

Rahoton yace Australia, Ingila da Canada da Amurka su suka fi amfana nesa ba kusa ba wajen daukar likitoci daga kasashen waje.

Masu binciken sun yi kira ga kasashen dake cin gajiyar likitocin, su zuba jari a fannin horas da ma’aikatan kiwon lafiya a kasashen da suke dauke musu likitoci, kamar yadda sharadin hukumar kiwon lafiya ta MDD kan da’ar daukar ma’aikatan kiwon lafiya daga ketare ya ayyana.

Sharadin hukumar ya tsawata kan daukan ma’aikatan kiwon lafiya daga kasashe masu tasowa dake fuskantar karancin ma’aikatan kiwon lafiya. Haka kuma tayi kira ga kasahe masu arziki su bada tallafin kudi ga kasashe matalauta, wadanda kaurace-kauracen likitocin da wasu ma’aikatan kiwon lafiya ta shafa.

Wan nan sharadi yana da muhimmancin gaske ga kasashen Afirka dake kudu da Hamadan Sahara wadan da suke fuskantar karancin likitoci da kuma yawan yaduwar cututtuka kamar su kanjamau, tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro na Malaria.

XS
SM
MD
LG