Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Shugan Amurka Bush Da Uwargidansa Zasu Kai Ziyara Afirka

George W. Bush da Laura Bush suke ziyarar kamfanin A to Z textile mills, wadda ke sarrafa magungunan yaki da cutar zazzabin cizon sauro.
George W. Bush da Laura Bush suke ziyarar kamfanin A to Z textile mills, wadda ke sarrafa magungunan yaki da cutar zazzabin cizon sauro.

Tsohon shugaban Amurka George W. Bush zai kai ziyara Afirka cikin watan gobe, domin ya kara jaddada shirye shirye da ake gudanarwa na yaki da cutar kanjamau da Malaria.

Tsohon shugaban Amurka George W. Bush zai kai ziyara Afirka cikin watan gobe, domin ya kara jaddada shirye shirye da ake gudanarwa na yaki da cutar kanjamau da Malaria.

Tsohon shugaban na Amurka da uwargidansa Laura Bush, zasu ziyaraci kasashen Tanzania, da Zambia, da Habasha, daga ranar 1-5 ga watan Disemba.

A yayinda suke nahiyar, tsohon shugaban da uwargidansa zasu tallata da kuma karfafa shiryen yaki da cututtuka da aka fara gudanarwa zamanin yana mulki, da kuma gidauniyarsa take kara bada tallafi akai.

A zamanin yana mulki tsakanin 2001-2009,Mr.Bush ya kaddamar da shirye shirye kan kudi dala milyan dubu 60 domin yaki da cututtukan kanjamau, zazzabin cizon sauro, da kuma tarin fuka a fadin Duniya baki daya. Galibin kudaden an bada su ne a Afirka.

Shugaba Barack Obama yana ci gaba da goyon bayan shirin kiwon lafiya da shugaba Bush ya fara, mai lakanin PEPFAR, wadda ya bada karfi wajen yaki da cutar kanjamau.

Haka kuma yayinda suke Afirka cibiyar aikace aikace ta Mr. Bush, tace tsohon shugaban da uwargidansa, zasu yi wata gagarumar shela, kan sabbin hanyoyin hana kamuwa da cutar kansa.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG