Accessibility links

Shugabannin Mulkin Sojin Misra za su Kafa Sabuwar Gwamnati

  • Ibrahim Garba

Cincirindon masu zanga-zanga a Misra

Shugabannin gwamnatin mulkin sojin Misra sun amince su kafa

Shugabannin gwamnatin mulkin sojin Misra sun amince su kafa sabuwar gwamnati tare da alkawarin mika ragamar iko ga wata hukumar fararen hula zuwa watan Yulin 2012.

Shugaban Majalisar Koli ta gwamnatin sojin, Mohammad Tantawi ne ya yi sanarwar, a wani jawabinsa da aka yada ta gidan talabijin da yammacin jiya Talata, bayan kammala taron tattauna rikicin kasar da kungiyoyin siyasa dabam-dabam. Ya ce ya amince da murabus din majalisar ministoci karkashin shugabancin Firayim Minista Essam Sharaf, to amman wai zata cigaba da kasancewa har sai an kafa sabuwar gwamnati.

Shugabannin mulkin sojin su ka ce a shirye su ke su gudanar da zaben raba gardama kan mika ragamar iko nan da nan, muddun ya zama dole. Sun kuma yi alkawarin fara shirin gudanar da zaben majalisar dokoki kamar yadda aka tsara ran 28 ga watan Nowumba, a kuma gudanar da na shugaban kasa kafin watan Yulin 2012.

Dubun dubatan masu zanga-zangar da su ka hallara a dandalin Tahrir, sun bayyana bacin ransu game da sanarwar ta Tantawi, su na cewa su fa so su ke a kawo karshen mulkin soji ba tare da bata lokaci ba. Wasu ma sun yi ta cewa ya sauka.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG