Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Ma'aikatan Gwamnatin Jihar Katsina Suna Maka Gwamnatin Jihar Kotu


Ma’aikatan kananan hukumomi a jihar Katsina fiye da dari shida ne suka gurfanar da gwamnatin jihar a gaban kotun kula da hakkokin ma’aikata ta Najeriya dake Kano saboda dakatar da albashin su da ta yi kimanin watanni ashirin da suka gabata, suna kuma neman diyyar naira miliyan dari biyar.

Tun a watan Afrilun bara ne gwamnatin jihar ta Katsina ta bada umurnin dakatar da albashin wasu daga cikin ma’aikatan dake aiki a karkashin majalisun kananan hukumomi talatin da hudu na jihar saboda zargin kauracewa wuraren ayyukan su.

Wadanda wannan matakin ya shafa sun kai kimanin dari shida da goma sha biyar.

Sai dai ma’aikatan sun musanta wannan ikirarin na gwamnati. Suna masu fadin cewa, gwamnatin na neman muzgunawa rayuwarsu ne kawai.

Bayan duk wani yunkuri na daidaitawa tsakanin bangarorin biyu ya ci tura, ma’aikatan sun gabatar da batun ga kotun kula da hakkokin ma’aikata ta tarayya dake nan Kano, domin ta sa gwamnatin jihar Katsina ta cigaba da biyan su albashi kuma ta basu ariya na watanni ashirin da suka gabata.

Sunayen ma’aikata biyar ne dai ke jikin takardar karar a matsayin wakilan sauran dari shida da goma, al’amarin da ya sanya lauyan gwamnati Barrista Abu Umar ke cewa, tunda ma’aikatan biyar sun nuna kananan hukumomin da suka dauke su aiki, ya kamata a zayyana sunayen sauran ma’aikatan don kotu ta san da su.

Sai dai lauyan dake kare ma’aikatan Barrista Kamalu Umar ya yi martani akan haka, ya ce ba haka batun yake ba, saboda dokar kotu ta bada wannan damar.

Yanzu haka dai alkalin kotun kula da hakkokin ma’aikatan ta Kano mai shari’a E.D Esele ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 7 ga watan gobe na Disamba.

Ga karin bayani cikin Sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG