Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Manyan 'Yan Adawa Sun Koma Jam'iyyar PNDS Mai Mulkin Niger


A janhuriyar Niger, jam’iyyar PNDS mai mulki ta yi na’am da wasu gaggan ‘yan adawa da suka sauya sheka a karshen makon da ya gabata.

Ta hanyar wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban kasar Niger da aka wallafa a shafin Facebook a karshen makon da ya gabata ne jama’a suka samu labarin ficewar Dr. Adal Rhoubeid daga sahun ‘yan adawa har ma shugaban ya bashi mukamin mashawarci na musamman a fadarsa, abinda galibin jama’a ke kallonsa tamkar na ba-zata saboda yadda wannan dan siyasar ya yi fice wajen caccakar gwamnatin Renaissance.

Abdoulmoumouni Ousman, na daga cikin abokan tafiyarsa a kawancen FPN na ‘yan adawa. Yace su ba za su jefa masa dutse ba. Za su ci gaba da gwagwarmaya. A cewarsa dama akwai mutanen da za su shigo, akwai kuma wadanda za su fice kamar yadda shugabansu ya yi.

Domin jin dalilin wannan canza shekar, shugaban jam’iyyar MDR Tarna Dr. Adal Roubeid, a wata hira ta wayar tarho da sashen hausa na muryar Amurka, ya ce yana cikin zaman makoki a inda ya ke saboda haka ba zai iya magana ba. To amma ya fadawa abokansa na FPN cewa shi ya fita daga jam’iyyarsu ne kawai ba tare da basu wata hujja ba. Amma abokan nasa sun ce talakawa ya kamata ya shaidawa ficewarsa da kuma shigarsa gwamnati. A cewarsu wani yunkuri ne na kashe adawa a kasar ta Niger.

Jam’iyyar Moden Lumana dake matsayin jagorar jam’iyyun adawar Niger ma ta fuskanci ballewar daya daga cikin kusoshin da suka kafata, wanda ake kira Ali Gaza Gaza, sai dai shi ma bai so yin furici akan wannan matakin nasa ba ballanatana a ji hujojinsa. Amma duk da haka wani kakakin jami’yar Bana Ibrahim na cewa ba su yi mamakin hakan ba. Ya ce su ma sun san wasu mutanen da suke tare da su ta kansu su keyi. A cewarsa shi Ali Gaza Gaza, duk da yana cikinsu wajen shekara hudu amma ba’a ganinsa a yawancin taronsu.

A tsawon shekaru 8 na mulkin Niger jam’iyyar PNDS Tarayya ta fuskanci suka daga ‘yan hamayya wadanda ke mata kallon matattarar mahandama da ‘yan babakere. Saboda haka sauya shekar ‘yan adawa a yau ya sa wani jigon jam'iyyar PNDS, Adamou Manzo cewar "akwai lokacin da mutum zai yi maka adawa, mugunyar adawa amma kuma daga baya sai ya lura abun da ya yi ba dai dai ba ne.” A cewarsa, su ‘yan adawar da suka yi watsi da adawa sun gane kuskurensu ne suka dawo cikin jam’iyyar PNDS mai mulki. Injishi sai a godewa Allah.

A saurari rahoton Souley Barma

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Facebook Forum

Labarai masu alaka

XS
SM
MD
LG