Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Masu Kada Kuri'a a Nijer Sun Yi Watsi Da Matakan Kariyar COVID-19


Tun da karfe 8 na safiyar yau Lahadi 27 ga watan Disamba ne aka bude yawancin rumfunan zabe a jamhuriyar Nijer don zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, yayin da masu kada kuri’a suka yi dafifi don zuwa kada kuri’unsu.

A birnin Yamai, Dosso, da Tillaberi rahotanni sun bayyana cewa komai na tafiya daidai kuma an baza jami’an tsaro a ko’ina don tabbatar da doka da oda a wuraren zaben.

A birnin Damagaram ma haka zancen ya ke, kusan a lokaci guda aka bude rumfunan zabe kuma komai na tafiya daidai. Yankin Diffa, da ya dade ya na fama da tashin hankalin ‘yan ta’adda, an samu rahoton jin harbe-harbe a daren ranar Asabar 26 ga watan Disamba.

A garin Bilma da ke yankin Agadez, mutane da yawa sun fito zaben musamman mata, haka kuma a jihar Maradi.

Shugaban hukumar zaben Birni N’Konni, ya ce an tura jami’an tsaro a yankin Bazazzaga da aka ce an ga wasu mutane akan babura suna zagaye-zagaye lamarin da ya kawo fargaba a tsakanin al’uma, a wata mazabar sabon gari da ke yankin kuma an kama wasu mutane da tarin katunan zabe.

Ana gudanar da babban zaben ne dai a daidai lokacin da ake fama da annobar cutar COVID-19 da ta kama mutane 3,057 a kasar da ke yammacin nahiyar Afrika. Rahotanni da ke fitowa daga wasu rumfunan zaben kasar sun bayyana cewa wasu masu kada kuri’a ba sa kiyaye matakan da aka sanya na kariya daga cutar kamar amfani da takunkumin rufe hanci da baki da kuma yin nesa-nesa da juna.

TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hukumomi Sun Fara Shirin Bada Gudumawar Jini A Fadin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG