Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Niger: Kungiyoyi Na Ci Gaba Da Jan Hankali Kan Zaman Lafiya


Harabar Hukumar Zabe Ta Jamhuriyar Nijar CENI
Harabar Hukumar Zabe Ta Jamhuriyar Nijar CENI

A yayin da ya rage ‘yan sa’oi kadan a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasar Nijer hade da na ‘yan majalisar dokoki, kungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da kara jan hankulan jama’a don ganin komai ya gudana cikin kwanciyar hankali.

‘Yan takara akalla 30 ne ke shirin fafatawa da nufin dare kujerar shugabancin kasar Nijer a zaben ranar Lahadi 27 ga watan Disamba yayin da wasu dubban ‘yan takara daga jam’iyyun siyasa dabam-daban ke fatan samun yardar jama’a don shiga zauren majalisar dokokin kasa mai kujerun wakilci 171, sabili kenan kungiyoyin sa ido wadanda suka hada da RJRN da MJCPS da CICOPROD ke kara yin kira ga ‘yan siyasa da su kasance masu nuna halin dattako a tsawon wannan lokaci mai matukar muhimmanci. Kamar yadda Anda Moussa Garba, kakakin wannan hadaka ya shaida.

Amfani da matasa a irin wannan lokaci na gudanar da zabe wani al’amari ne da ya zama ruwan dare a kasashen nahiyar Afrika, a saboda haka wadannan kungiyoyi ke yi wa matasan Nijer hannunka mai sanda.

A jajibirin wannan zabe wata tawagar hadin gwiwar hukumar CENI da hukumar raya karkara ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNDP ko PNUD ta kira taron fadakarwa a birnin Yamai bayan kammala zagayen illahirin jihohin Nijer da nufin tunatar da mata da matasa muhimmancin zabe da matsayin da suke da shi a irin wannan lokaci na cashe aya da tsakuwa a tsakanin ‘yan siyasa. Jami’a a hukumar zabe, kusa kuma a kungiyoyin kare hakkin mata Mme Katambe Mariama, na daga cikin wadanda suka shirya wannan zama.

Tuni dai aka rufe yakin neman zabe da karfe 12 na daren juma’a 25 ga watan Disamba a fadin wannan kasa, yayin da a wunin ranar Asabar wasu mazaunan Yamai ke tafiya yankunan da suka yi rajista domin kada kuri’unsu a ranar Lahadi 27 ga watan nan. Hukumar zabe ta ce a bisa ka’ida rumfunan zabe zasu bude daga karfe 8 na safe zuwa 7 na yamma agogon wannan kasa.

Saurari cikakken rahoton Souley Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

XS
SM
MD
LG