Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matakan Haraji Da Ake Neman Dauka A Nijer Sun Janyo Cece-kuce


A Janhuriyar Nijer tsarin kasafin kudaden da gwamnatin kasar ta gabatarwa majalissar dokokin kasar ya haddasa tayar da jijiyoyin wuya a wajen ‘yan adawa da kungiyoyin kare hakkin jama’a, saboda a cewar su tsarin kasafin na shekarar 2018 na kunshe da wasu dokokin tauye rayuwar talakawa.

Shirin karbar haraji akan wasu ababen da a can da ba su da haraji da yinkurin farfado da wasu dokokin da gwamnatocin da suka shude suka jingine saboda wasu dalilai, shi ke kara harzuka jama’a da wasu kungiyoyin dake fafutikar kare hakkokin jama’a kamar MPCR ta Nuhu Muhammadu Arzika, da suka fara kalubalantar wadannna matakan da suke gani za su iya jefa jama’a a cikin kuncin rayuwa.

Domin haska fitila akan sabuwar dokar harajin dake shan suka daga rukunonin al’umma, missali karbar haraji daga dukiyar da mamaci ya barwa magadansa, ministan kudi Hassoumi Massaoudou ya hallara a zauren majalissa a jiya Laraba, to amma dan majalisar dokoki na bangaren adawa, Sumana Sanda ya ce basu gamsu da bayanin da aka yi masu ba.

Sai dai shugaban kwamitin kula da sha’anin kudi a majalisar dokokin kasar, honorable Adamu Namata, ya ce ba za su amince da abinda zai jefa jama’a ko kasar cikin wani mummunan hali ba, don haka a shirye suke su saurari ra’ayoyin jama’a da na kungiyoyin kare hakkokin bil’adama.

Kungiyoyin farafen hula dake adawa da wannan sabuwar dokar ta haraji, sun kudiri aniyar gudanar da zanga-zanga domin tilastawa gwamnati ta canza ra’ayi. Matakin da masu rinjaye a majalissar ke ganin rashin cancantarsa.

Wakilin muryar Amurka Sule Mumuni Barma na da Karin bayani a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG