Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mutane Da Ake Kyautata Zaton ‘Yan Bindiga Ne Sun Kashe Mutane 25 A Kudu Maso Yammacin Nijar


‘Yan bindiga
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:15 0:00

‘Yan bindiga

Ana kyautata zaton wasu ‘yan bindiga sun kashe akalla mutane 25 a yankin kudu maso yammacin jamhuriyar Nijar, kamar yadda gwamnatin kasar ta sanar a ranar Laraba.

An kona gine-gine a harin da aka kai a farkon makon nan kusa da kauyen Bakorat da ke kan iyaka da kasar Mali, in ji ministan cikin gidan kasar, Alkache Alhada a cikin wata sanarwa da ya fitar. Gwamnati ta ce ana ci gaba da gudanar da aikin tsaro a yankin.

Wannan dai shi ne daya daga cikin jerin tashe-tashen hankula na baya bayan nan masu nasaba da al-Qaida da kuma kungiyar IS a yankin yammacin Afirka da ke fama da rikice-rikece musamman kan iyakar kasar. A farkon wannan watan ne wasu da ake zargin masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama ne suka yi wa wata tawagar kare kai a yammacin Nijar kwanton bauna inda suka kashe mutane 69 a cikin watan Maris, wasu 'yan bindiga kan babura suka kashe mutane 137 da suka kai hari kan wasu kauyukan da ke kan iyaka.

Yayin da babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin na wannan makon, al-Qaida ta fi fice a wannan yanki na Nijar domin ta shafe shekaru da dama tana gudanar da ayyukanta a can, in ji masana kan rikice-rikice.

Hare-haren na nuni da yadda ake ci gaba da samun karuwar tashe-tashen hankula a yankin Sahel, yankin kudu da hamadar Sahara, in ji Laith Alkhouri, shugaban wani kamfanin liken asiri, Intelonyx Intelligence Advisory.

Ya kara da cewa, "Yana kara nuna rashin matakan tsaro kan iyakoki da ke sanadiyar kungiyoyin ta'addanci kamar su al-Qaida da ISIS, ke fafutukar neman rinjaye, da ma damar fadadawa,".

XS
SM
MD
LG