Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Sandan Najeriya Ya Fasa Kwai - Kashi na Daya


Yayin da yake zantawa da wakilin Muryar Amurka wani dan sandan kwantar da tarzoma wato MOPOL ya bayyana irin rashin adalci da rashin kulawa da shugabanninsu ke nuna masu a wurin aiki, musamman ma a arewa masu gabashin kasar inda suke fafatawa da mayakan Boko Haram.

MOPOL MANU: A yau ina shekaru 14 kennan ina aikin dan sanda, sannan nayi watanni 5 a Maiduguri. Nayi aiki a Kwanduga, na kuma yi aiki a Gambarau, na yi aiki a Bama. Wani lokaci idan aka debe mu, a tafi da mu. Abunda ya faru, ranar 5 ga wata (Mayu), an same mu, an kawo mana hari a Gambarau. Muna zaune, sai muka ga motocin soja wato APC da kuma kayan Soja, suka zo, sukayi “surrender”, muka gaisa dasu. Bayan mun gama, sai suka ce sunzo wajenmu “reinforcement” ne. Muka ce yana da kyau haka, Allah Ya bi tare da mu.

Ba’a yi minti biyu ba, sai muka ji sun fara salati, sai muka ji harbi ya fara tashi. Aka samu ‘ya’yanmu, mu “Mobile” da muke a wurin, aka kashe mutum 13 a wurin. Abunda ke bamu bakin ciki shine a yau duniyannan, na fito inyi magana, don abunda ya faru da ‘yan uwana a wajen aiki. Na daya, yarannan wadanda aka kashe su, babu wanda ya taso zuwa. Mun yi kiran shugabanninmu, muka ce ga abinda ya faru, basu iya sun zo ba, har bayan kwanaki biyu, na uku sai suka zo. An kwashe yarannan da cewa za’a kaisu asibiti mutuwari, domin a saka musu maganin da zai hana gawarsu rubewa. Abun bakin ciki shine, a yau idan kana aikinnnan, kana da rai, ka zama mutum, wanda manyanmu zasu yi amfani da kai, su dauki abunda suke so a cikin rayuwarsu. Amma yau idan ka kwanta dama kai ba komai bane a gabansu. Ka zama abun banza, za’a wulakantar da gawarka, za’a wulakantar da gangar jikin da Allah Ya shirya. Gwamna (Borno) ya bada kudi a sakawa gawarwakin magani, amma shi kwamishinan ‘yan sanda Jihar Borno, abunda bai iya yi ba kennan.
Sannan munje zamu kwashi gawarwakinnan aka ce babu, ba’a biya kudaden ba, kuma gawarwakin yaran sun riga sun lalace. To wannan abun ya bamu bakin ciki. Bamu san ko shi Gwamnan Borno yana sane da abunda ke faruwa ba. Muhimmin abunda ke damun mu a wannan aikin shine, idan kana da yaro a gidanka, baza ka aiki wannan yaro zuwa gona, ba tare da garma a hannunsa ba, ba tare da ko adda ko wani abu a hannunsa ba, ba tare da ruwan sha a hannunsa ba, domin idan yaje wannan gonar, ba zai iya yi maka aikin da kake so ba, domin baka bashi kayayyakin aiki ba.

Jama’ar nan suna zuwa mana da dubban harsashi a hannayensu, mu kuma muna tafiya da guda talatin. Idan ka samu guda sittin, to ta yiwu ka bada cin hanci, kamin a baka guda sittin. Abunda ake bayarwa kaje kayi aiki da shi kennan. To yaya mutum yana da harsashi kusan dubu a hannunsa, kai kuma kana da 30, me zakayi da shi? WalLahi ina gaya maka, ina gayawa jama’a, wannan abunda yaka faruwa bai gagara ba. Amma manyan shugabanninmu suke zaluntar wannan kasar. Basa so wannan fada ya kare, an mayar dashi abunda ake kasuwa da shi, domin idan ya kare, kudin da ake kashewa baza su samu kuma ba. Muna aikinnan yau da yunwa. Babu komai, babu albashi, albashinka ma wanda ya kamata ka baiwa ‘ya’yanka a gida shine kake ci. Kuma ka fito domin ka tsare kasarka, ka yaki abunda yake cikin kasarka. An bar ka da yunwa. Idan ma ana bayarwa, to mu na kasa bama gani, yana tsayawa a sama ne. Giwa ya taka rakumi, tsawansa ya riga ya rufe na rakumi, babu yanda za’a yi yayi motsi, saboda haka gwamma mu fito mu gayawa duniya abinda ke faruwa. Abunda ke faruwa a yau kennan. A yanzun ma idan ka koma, kaje “zone 4” idan ka tafi zaka ga ba’a biya albashi ba tun daga wata daya babu kudin gida a cikinsa, ga yara suna makaranta, ka karan kanka, yaya zaka ci da kanka? ‘Ya’yanka me zasu ci a gida? To kaga wadannan abubuwa muna bakin ciki, azzalumai suna zaluntarmu da yawa. Suna zambarmu cikin aminci, amma babu mai iya yi musu magana.


Bayan jin wannan ne, Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tuntubi tsohon Sfeton 'yan Sandan Najeriya Muhammadu Gambo Jumeta, wanda yace wannan lamari na ta'addanci bakon abu ne ga 'yan sanda.

JUMETA: Wannan batu, baza a iya daukewa wata kungiya ko jama'a ko wata jama'a hakkin abunda ke faruwa ba. Shi dan sanda babu shakka, abu ne wanda yake basuyi tsammani zai kai ga haka ba, kuma basu shirya wa wannan abun ya faru ba sam. Don haka ina gani ya kamata, a samu matakalai na tsaka-tsaki, wanda za'a zauna ayi maganar kawo sulhu da fahimtar juna tsakanin gwamnati da 'yan adawa, da duk wanda keda halin a sasanta.


Wannan shine kashin farko na hira da Muryar Amurka yayi da dan sanda. A kwanaki masu zuwa, zamu kawo ragowar hirar.

XS
SM
MD
LG