Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Najeriya Sun Yi Tsokaci Akan Jawabin BanKwana Na Shugaba Obama


Shugaban Amurka Barack Obama yayinda yake yiwa Amurkawa jawabin bankwana
Shugaban Amurka Barack Obama yayinda yake yiwa Amurkawa jawabin bankwana

Kodayake Shugaban Amurka Barack Obama mai barin gado ya yiwa Amurkawa jawabin bankwana ne amma jawabin nasa ya dauki hankulan mutanen kasashen duniya daban daban cikinsu har da kasar Najeriya.

Wasu 'yan Najeriya da suka zanta da Muryar Amurka sun yiwa shugaban fatan alheri tare da kiran nasu shugabannin su yi koyi da shugaba Barack Obama, su yi mulki da gaskiya da adalci.

Wanda yayi magana da farko yace ko shakka babu suna alfahari dashi kasancewarsa bakin fatar farko da ya shugabanci Amurka kuma kawo yanzu babu wani abun asha da aka sani yayi.

Wani bayan ya yiwa shugaba Obama fatan alheri ya kira shugabannin Afirka musamman Najeriya su yi la'akari da yadda Obama yayi mulki kuma kafin ya sauka har ya yiwa 'yan kasa bayanin abubuwan da yayi. Inji dan talikin, irin wannan hali na Obama abun koyi ne.

Baicin kiran shugabannin Afirka su yi koyi da Obama, 'yan Najeriya sun kara kiran shugaba mai jiran gado Donald Trump da yayi koyi da Obama. Yayi mulki ba tare da nuna banbancin jinsi ko na addini ba

Inji ta bakin wani mai magana yace shugaba Obama zai sauka ba tare da wawure dukiyar jama'a ba kamar yadda shugabanin Afirka keyi. Yawancin shugabannin Afirka burinsu ne 'ya'yansu su gajesu. Haka kuma Obama bai tada wani yaki ba ,maimakon haka ma warware yaki ya dinga yi.

Ga rahoton Babangida Jibril da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

XS
SM
MD
LG