Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Waye Zai Lashe Zaben Shugaban Kasar Senegal?


Yanzu 'yan takara hudu ne suke kalubalantar shugaban kasar Senegal Macky Salls a Zaben shugaban kasar da aka yi jiya Lahadi, cikin kwanciyar hankali da lumana.

An fara kidayar kuri’u a kasar Senegal bayan an yi zaben Shugaban kasa cikin kwanciyar hankali a jiya Lahadi.

A cewar hukumar zaben kasar CENA, an rufe wuraren zaben da karfe 6 agogon kasar, inda ake sa ran fara samun sakamako na wucin gadi a yau Litinin ko gobe Talata.

Bayan sati uku ana yakin neman zabe, masu jefa kuri’a sun kafa dogayen layuka tun da safiyar jiya Lahadi kodai suna goyon bayan shugaba mai ci Macky Salls da ya ke neman a sake zabarsa ko kuma a canja shi da daya daga cikin mutum hudu da suke kalubalantarsa, Idrissa Seck, Ousmane Sonko, Madicke Niang ko Issa Sall.

An dai gudanar da zaben lami lafiya kuma babu wasu manyan matsaloli a lokacin zaben, Doudou Ndir, shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta Senegal (CENA) ya fadawa taron manema labarai.

“Abubuwan da muka gani sun nuna gaba daya an gudanar da zaben a cikin kyakkyawan yanayi, kwanciyar hakali, zaman lafiya,” Ndir ya ce.

Shugaba Sall dan shekaru 56 da haihuwa ya kada kuri’arsa a garinsu na Fatick a jiya Lahadi. “yana fatan cewa a karshen ranar yau, mutanen Senegal za su zama su suka lashe, kamar yadda ya fada bayan da ya jefa kuri’arsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG