Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka Colin Powell Ya Mutu Sanadiyyar COVID-19


Marigayi Colin Powell
Marigayi Colin Powell

Powell ya rike mukamin sakataren harkokin wajen Amurka a tsakanin shekarun 2001 zuwa 2005 a wa’adin farko na shugaba George W. Bush.

Janar Colin Powell, bakar fata na farko da ya rike mukamin Sakataren harkokin wajen Amurka ya mutu. Shekarunsa 84.

Powell wanda har ila yau shi ne bakar fata na farko da rike mukamin shugaban hafsan hafsoshin sojin Amurka ya rasu ne sanadiyyar cutar COVID-19 a ranar Litinin.

Iyalansa ne suka bayyana rasuwar tasa a shafin Facebook, suna masu cewa “mun yi rashin miji nagari, uba, kaka kuma mashahurin Ba’amurke.”

Iyalan mamacin sun ce Powell ya yi cikakkiyar allurar riga-kafin cutar ta COVID tun gabanin ya fara rashin lafiya.

Sun kuma mika godiyarsu ga ma’aikatan asibitin Walter Reed na kasa da ke wajen birnin Washington, “bisa irin kulawa da suka nunawa Powell,” a lokacin yana jinya.

Powell ya rike mukamin sakataren harkokin wajen Amurka a tsakanin shekrun 2001 zuwa 2005 a wa’adin farko na shugaba George W. Bush.

XS
SM
MD
LG