Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Turai Sun Mayar Da Martani A Kan Kashe Kashoggi


Daga hagu, Shugaban Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Emmanuel Macron
Daga hagu, Shugaban Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Emmanuel Macron

Kasashen Faransa da Jamus sun yi Allah wadai da kashe dan jaridar Saudiya Kamal Kashoogi a cikin ofishin jakadancin Saudi Arabia a Istanbul.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya yi kira a jiya Asabar a kan gudan da sahihi kuma cikakken bincike domin gano takamaiman wadanda suka kashe Kashoogi. Le Drain ya kuma ce duk wanda aka same shi da laifin aikata wannan danyen aiki, a hukunta shi bisa ga laifinsa.

Shugaban Jamus Angela Merkel da ministan harkokin wajenta Heiko Maas sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa suna Allah wadai da wannan kisar da kakkausa lafazi. Sun ci gaba da cewa, suna sa ran Saudi Arabia zata tabbatar da gaskiya wurin bada cikakken bayani a kan mutuwar Kashoogi, kana suka ce bayanai da aka fitar a kan wannan batu basu isa ba.

Merkel tace babu wani bayani mai gamsarwa da aka yi kuma yakamata a yi mana bayani cikakke.

Babban jami’ar shirye shiryen harkokin wajen Kungiyar Tarayyar Turai Frederica Mogherini ta fada a jiya Asabar cewa yanayin da aka kashe Kashoogi babban abin damuwa ne, ta kuma yi kira ga tabbatar da binciken kwakkwaf da gaskiya da adalci a kan wannan batu.

Kalaman shugabannin Turan na mayar da martani ne a kan sanarwar Saudi Arabia a kan Kashoogi da ya bace tun lokacin da ya shiga ofishin jakadancin Saudiyar a Istanbul a ranar biyu ga wannan watan Oktoba, cewa ya mutu a cikin ofishin jakadancinta bayan ya yi fada da mutane da ya samu a wurin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG