Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Aikin Shinfida Layin Dogo Na Kano -Maradi Ya Shafi Gidaje Da Sana’o’in Al’umma


Lokaci da Buhari ya kaddamar da aikin layin Dogo a Kano (Hoto: Fadar shugaban kasa)
Lokaci da Buhari ya kaddamar da aikin layin Dogo a Kano (Hoto: Fadar shugaban kasa)

Tun a farkon shekara ta 2022 ne gwamnatin Najeriya ta amince tare da ba da kwangilar gina layin dogo daga Dutse zuwa Kano da kuma Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar, da nufin habaka harkokin sufuri da na hada-hadar kasuwanci a tsakanin Najeriya da Nijar.

Dubban daruruwan magidanta da iyalai a Kano wadanda aikin shinfida layin dogo daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar ya shafi gidaje da wuraren sana’o’insu sun zargi jami’an ma’aikatar harkokin sufuri ta Najeriya da jefa su cikin yanayin rashin tabbas fiye da shekara guda bayan an zana lambar rusa gine-ginen su kuma aka umarci su dakatar da yin komai.

Tun a farkon shekara ta 2022 ne gwamnatin Najeriya ta amince tare da ba da kwangilar gina layin dogo daga Dutse zuwa Kano da kuma Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar da nufin habaka harkokin sufuri da na hada-hadar kasuwanci a tsakanin Najeriya da Nijar.

Ko da yake daukacin al’umomin da ke wannan nahiya sun yi maraba da wannan yunkuri, amma wasu dubban magidanta a Kano da aikin ya keta ta matsugunnansu na cikin halin rashin tabbas.

Alhaji Bashir Mahdi Muhktar shine kakakin al’umomin da wannan aiki zai bi ta muhallin su. Yace, “An zo an auna guraren mu, aka ce wannan aikin na hanyar jirgin kasa zai biyo ta kan su, a wancan lokaci aka dakatar da mu baki daya. Mai aiki , mai sana’a, mai noma, mai gidan gona, duk aka nemi kowa ya dakata. Aka kiyasta guraren mu aka bamu takardu kuma aka shardanta mana cewa kowa ya dakata kasa da watanni uku za’a sallami kowa.”

Malama Bilkisu Auwalu Umar wata uwar marayu ce da ta ce mijinta ya bar musu gida kuma a cikin wani sashi na gidan ne take kiwon kaji domin ciyar da marayunta. “Wallahi mun shiga wani hali ni da marayun yarana, sun ba mu tabbacin cewa, watanni uku masu zuwa za su zo su ci gaba da aiki, don haka kowa ya dakata da abin da yake yi a wuraren da aka yiwa lamba, yanzu fiye da shekara guda babu wanda yace da mu uffan, dangane da haka komai nawa ya lalace;”

Kimanin magidanta dubu goma ne aka kiyasta wannan aikin na layin dogo zai shafa, ciki har da Usama Abubakar, wani matashi da aka daga bikin auren sa har sau uku sanadiyyar wannan aiki na layin dogo da aka ce zai bi ta unguwar da yake gina gida.

Da muka tuntubi sakataren labaru na ma’aikatar Malam Zakari ya ce ba za’a ce da wadanna al’umomi komai ba har sai ma’ikatar ta kammala abin da ke gabanta, kuma ko da lokacin yayi minista ne zai sanar da makomar mutanen.

Saurari rahoton:

Yadda Aikin Shinfida Layin Dogo Daga Kano Zuwa Maradi Ya Shafi Gidaje Da Sana’o’in Al’ummar Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG