Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Taron Bita Ga Jami’an Hisba Kan Muhimmancin Kare Mata Da Yara A Iyali


Taron Hisbah
Taron Hisbah

An kammala taron bita da kara wa juna sani na yini uku a Kano ga kwamandoji da sauran manyan Jami’an hukumomin Hisbah na jihohi 6 a arewa maso yammacin Najeriya.

Taron ya maida hankali ne akan dabaru da hikimomin tunkarar kalubalen zamantakewar gida da harkokin ma'aurata, musamman sha’anin cin zarafin mata da kananan yara.

Wakilai daga hukumomin Hizaba na jihohin Kano da Katsina da Kebbi da Sokoto da Jigawa da kuma Zamfara ne suka halarci taron, inda masana dokokin da suka shafi yaki da cin zarafin mata da yara da kuma mahangar shari’ar Musulinci akan wadannan batutuwa suka gabatar da makaloli kana daga bisani aka tafka mahawara a zauren taron.

Malam Abdullahi Abba Maimaje, mataimakin kwamandan Hizbah na jihar Katsina ya ce sun koyi sabbin abubuwa da yawa, musamman yadda ya kamata su yi amfani da dokokin kasa wajen gudanar da ayyukansu cikin sauki da nasara.

Mahalarta taron dai sun lura cewa, ala’adu da rashin wayewa da kuma talauci na cikin manyan abubuwan da ke mayar da hannun agogo baya ga kusan dukkannin wani yunkuri na magance matsalar cin zarafin mata da yara a lardin arewacin Najeriya.

To amma Malam Ibrahim Dahiru Garki da ke zaman kwamandan hukumar Hizbah ta jihar Jigawa ya ce wannan matsala ta cin zarafin mata da yara ta kusa zuwa karshe, la’akati da sabuwar dokar yaki da cin zarafin mata da yara da jihar Jigawa ta samar a jihar, yana mai cewa, za su yi kokari su koyar da sauran jami’an su na Hizbah ilimin da suka samu a wurin taron bitar.

Taron karawa juna sani na Jami'an Hisba
Taron karawa juna sani na Jami'an Hisba

Cibiyar DRPC (Development Research Projects Center) mai bincike kan kyautata ala’amuran jama’a, bisa tallafin gidauniyar Ford Foundation da suka shirya taron sun ce za su ci gaba da sanya ido, domin horon ya yi tasirin ga sauran jami’an Hizba a jihohin 6 da suka halarci taron, kamar yadda Barr Umar Ahmad Umar jimi’i a cibiyar ta DRPC ke fadi, yana mai cewa, cibiyar zata aika wakilai da zasu sanya idanu a wuraren bada horon ga sauran jami’an Hizbah a matakin jihohi.

Ya ce Cibiyar ta DRPC ta shawarci kwamandojin hukumomin Hizbar da suka halarci taron su rinka amfani da lauyoyinsu kamar yadda ya kamata.

Baya ga bada irin wannan horo ga Jami’an Hizbah, Masu kula da lamura na ganin akwai bukatar kara kaimi wajen magance matsalar ala’du da talauci da akan fake da su wajen ci gaba da cin zarafin mata da yara a Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
XS
SM
MD
LG