Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Father Mbaka Ya Nema Kwangila A Wajen Buhari - Garba Shehu


Rev. Ejike Mbaka (Instagram/ rev.ejike mbaka)
Rev. Ejike Mbaka (Instagram/ rev.ejike mbaka)

"Father Mbaka ya nemi ya ga Buhari, amma abin mamaki da ya tashi zuwa, sai ya taho da wasu ‘yan kwangila uku, ya nemi a ba shi kwangila a matsayin sakayyar goyon bayan da ya nunawa Buhari.”

Fadar gwamnatin Najeriya ta mayar da martani, dangane da kiran da fitaccen malamin addinin Katolika Rev. Father Ejike Mbaka ya yi na cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a mulki ko a tsige shi.

A ranar Laraba Father Mbaka ya yi kira ga Buhari wanda ke mulkinsa a wa;adi na biyu, da ya sauka a ko kuma a tsige shi, saboda abin da ya kira gazawa da ya yi wajen kare rayukan al’uma.

“Ta ya ya mutane za su yi ta mutuwa, sannan babban mai tsaron kasa zai zauna ba tare da ya ce uffan ba.” Mbaka ya ce.

Sai dai cikin wata sanarwa da fadar ta fitar dauke da sa hannun kakakin Buhari Malam Garba Shehu a ranar Juma’a, fadar ta yi ikrarin cewa kwangila malamin addinin ya nema aka hana shi, dalili kenan da ya sa ya sauya goyon bayan da yake nunawa Buhari.

Kokarin jin ta bakin malamin addinin kan ikrarin gwamnatin ya cutura.

Sanarwar ta kara da cewa, “Father Mbaka ya nemi ya ga Buhari, amma abin mamaki da ya tashi zuwa, sai ya taho da wasu ‘yan kwangila uku. Amma duk da haka Buhari ya ce a bar su su shiga. Wani abin al’ajabi, sai Father Mbaka ya nemi a ba shi kwangila a matsayin sakayyar goyon bayan da ya nunawa Buhari.”

Karin bayani akan: Father Mbaka, Garba Shehu, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“Mutane da dama, za su yi mamakin cewa, bayan nuna goyon baya ga Shugaba Muhammadu Buhari sau biyu don ya samu nasara, Father Mbaka ya sauya matsayarsa, inda ya yi kira a gare shi da ya sauka a mulki.” Shehu ya ce.

Ya kara da cewa “duk wanda ya san shugaba Buhari, ya san ba ya kaucewa ka’ida a mu’amullar da ta shafi bada kwangila ko kuma wani sha’anin da ya shafi gwamnati. Hakan ya sa shugaba Buhari ya mika batun ga hukumar da ta dace kamar yadda shari’a ta shimfida.”

“Hakan ya sa a cikin fadar aka rufe maganar, domini dan hotuna da wannan bukata ta Mbaka ta fito baina jama’a, mabiyansa za su juya masa baya. Hakan ya sa aka ki fitar da wadannan bayanai, dalili kenan da ya sa Father Mbaka yake kumfar baki.

Wannan martani da fadar shugaban kasar ta fitar, ta bude wani sabon babin ce-ce-ku-ce da ake yi dangane matsayar da malamin addinin ya dauka.

XS
SM
MD
LG