Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Gwamnatinmu Zata Shawo Kan Matsalar Tsaro-Datti Baba Ahmed


Aliyu Mustapha da Datti Baba Ahmed a Abuja
Aliyu Mustapha da Datti Baba Ahmed a Abuja

Dan takarar Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya karkashin tutar Jam’iyar Labor, Yusuf Datti Baba Ahmed ya bayyana cewa cin hanci da rashawa na daya daga cikin dalilan da su ka haifar da matsalar tsaro a Najeriya.

A hirar su da shugaban Sashen Hausa, Aliyu Mustapha Sokoto, datti ya bayyana matakan da za su dauka na sauya lamuran da suke ciwa al’umma tuwo a kwarya idan suka sami shugabancin kasar. Ya kuma yi tsokaci kan rade rade da suka shafi takararsu.

Janyewar Takarar Peter Obi

Dangane da jita-jitar da ake yadawa cewa, Peter Obi zai janye takarar shugaban kasa, ya goyi bayan wani dantakara, Datti ya ce, babu kanshin gaskiya a wannan batun da ya bayyana a matsayin alamun karshen zamani da kuma abinda siyasa ta gada.

Bisa ga cewarshi, abinda ya sa wadansu ‘yan siyasa suke daukar irin wannan matakin yakin neman zabe ba wani abu bane illa firgita. Bisa ga cewarshi, firgita ta kan sa mutum ya yi wani abu na fitar hankali. Sai dai yace idan mai fada bashi da zurfin tunani, mai sauraro yana da shi. Yace daukar irin wadannan matakan yaudara ga ‘yan takara masu rauni ba bakon abu ba ne a siyasar Najeriya.

Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed
Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed

Addini

Da yake bayani kan siyasar bata suna, Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya bayyana irin rawar da ya taka a fannin raya addinin Musulunci biyo bayan zarge zarge da yakin neman zabe na batanci da ‘yan hamayya suka shiga inda suka rika yayata cewa, yana nisanta kansa da Musulmi da kuma Musulunci.

Yusuf Datti Baba Ahmed yace ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa bankin raya Musulunci bayanda ya gabatar da kuduri a shekara ta 2005, shekaru bayan wannan yunkurin ya kafe. Ya kuma ce, bankin ya taimaka gaya wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya. Ya yi misali da zuba jari da bankin ya yi a bankin Jaiz, wani bankin tsarin addinin Musulunci da ba a bada bashi da ruwa, banda haka kuma ya gina Masallatai da dama. Ya bayyana mamakin yadda siyasa za ta sa a yi watsi da dukan wannan kokari da yace fadin haka ya sabawa addinin Musulunci.

Dangane kuma da batun addinan 'yan takarar shugaban kasa, ya bayyana cewa, jam'iyar Labor ta tsaida su takara ne bisa cancanta da kishin kasa, ba bisa la'akari da addinan 'yan takarar ba. Ya kuma bada tabbacin cewa, zasu tafiyar da ayyukansu bisa wannan kwarewa da rike amana.

Yajin Aiki

Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, gwamnatinsu za ta magance matsalar yajin aiki a kasar musamman a fannin harkokin ilimi. Ya ce, bai goyi bayan wadanda ke cewa, malaman jami’oin da ke yajin aiki sun yi zari a bukatun da su ka gabatar wa gwamnati ba. Bisa ga cewarshi, idan akwai hali, kamata ya yi, a yi ninkin ba ninki kan abinda ake biyan jami’an tsaro da kuma malamai sabili da muhimmancin ayyukan da su ke yi ga al’umma da ci gaban kasa. Yace ba zai taba goyon bayan a wulakanta malamin makaranta ba.

Da aka tambaye shi abinda ya ke gani ya janyo cijewar tattaunawa tsakanin gwamnati da malaman makarantar sai ya bayyana cewa, “taurin kan gwamnati da rashin maida hankali, saboda abu ne da shugaban kasa da kanshi ya kamata ya zauna ya tabbatar an kashe wannan yajin aikin, kuma an dau matakin da ba za a sake yi ba.”

Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed
Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed

Ya bayyana cewa, idan suka kafa gwamnati, zai roki shugaban kasa Peter Obi ya zauna da kansa da kungiyar malaman jami’oin su cimma matsaya su kuma tsaida yarjejeniyar cewa ba zasu sake shiga yajin aiki ba na tsawon a kalla shekaru hudu. Bisa ga cewarsa, banda Najeriya, babu kasar da za a bari malaman jami’oi su shafe watanni hudu suna yajin aiki dalibai na zaune a gida kara zube.

Datti ya bayyana takaicin ganin wadanda yace kasar ba ta amfana da harkokinsu, “banda maida hannun agogo baya da haifar da tsadar rayuwa, su ka fi cin moriyar gwamnati.” Ya yi misali da yadda ake ba ‘yan kasuwa wadanda yace, ba su aikin komi sai saida Dala, kudin a sawwake daga babban bankin Najeriya, su dibi ribarsu, su kuma sa Naira ta kara faduwa. Yace banda su, akwai kuma wadanda suke taimakawa rashawa a harkar mai, ta wajen bada sassaucin mai da iri-irinsu.

Matsalar Tsaro

Dan takarar Mataimakin Shugaban kasar ya bayyana cewa, abu na farko da ya haifar da matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya shine cin hanci da rashawa da gwamnati ta kafu a kai, ta ke kuma rayuwa a kai. Na biyu, yanda ake gudanar da harkokin siyasar damokaradiya.

Yace, “tsaro samar da shi ake yi ba sayenshi ake yi ba. Bisa ga cewarshi, “dukan abinda za ka je kasuwa ka saya, sai ka kimanta hankali da kishi, da tsoron Allah…dukan wadannan uku basu ciki, saboda a sawo wa Najeriya ko kuma samar mata da tsaro, akwai sakaci, akwai aringizo daga wurin gwamnatin da ke kai...duk sayen kayan aikin da za a yi, akwai kazamar riba da ke samu, na daya, yawan kayan aikin ya ragu, na biyu kuma ingancinsa ya ragu. Kama daga abincin da soja zai ci a bakin yaki, zuwa makamai duk rashawa ta shiga. Sannan kuma idan aka koma baya, tun daga lokacin da ake daukar aiki, an shigar da sa rai, sai ‘yan’uwa, sai abokai da ‘ya’yansu, wadansu kuma sai sun ciro kudi sun saya. Idan kai ya lalace, ganganjiki zai bi.”

Bisa ga cewar Saneta Datti, gyaran Najeriya ba mawuyacin abu bane idan aka sami shugaban da zai cire son rai. Ya yi bayani da lokacin da gwamnoni suka fara daukar kudin al’umma suna biyan ‘yan banga domin cimma manufofin siyasa ba tare da la’akari da abinda wannan zai haifar ba. Yace wadanda aka rika amfani da su ne a baya domin cimma manufar siyasa, sanadin inda kasar ke ciki a halin yanzu.

Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed
Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed

Dangane da batun garkuwa da mutane da neman kudin fansa da ya fi muni a arewacin kasar, ya ce haka na faruwa ne sabili da rashin kishin shugabannin yankin, da talauci da ya yiwa al’ummar yankin katutu, da raunin ilimi, da kuma raunin imani da sauransu.

Ya dora alhakin matsalolin tsaron da ya hada da garkuwa da mutane kan sakacin gwamnati.

Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa

Dan takarar Mataimakin Shugaban Kasar ya bayyana cewa, idan jam’iyar Labor ta kafa gwamnati, mataki na farko da zata dauka na yaki da cin hanci da rashawa shine cire son rai. Bisa ga cewarshi, sun riga sun dauki duk wani matakin cire son rai, sun kuma kudurta cewa, idan abu ba halaliyarsu ba ne ba zasu sa kwadayi a kai ba. Ya bayyana cewa, banda wadatar zuci, shi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyar Peter Obi suna da abinda za su rufawa iyalansu asiri, kuma ba su dauki abokan tafiyar da su ke jira su hau mulki su azurta kansu ba.

Datti ya bayyana cewa, galibin wadanda suke gwamnatin Buhari sun shiga ne cikin matsanancin talauci wadansu da basusuka da ya sa da dai suka hau karagar mulki, babu abinda suka maida hankali a kai sai neman hanyar samun kudi, lamarin da yasa suka rika shiga neman dala suna sayarwa da ya yi sanadin faduwar darajar Naira da ake fama da shi a kasar. Bisa ga cewarshi, “wasu a gwamnatin Buhari da rarrafe su ka zo, wasu dauke da basusuka, wadansu sun yi caca sun dauki abinda duk ya rage a hannunsu sun kashe a siyasa, suna dawowa abu na farko da suka yi sai neman maida kudinsu.”.

Ya bayyana cewa, akasin abinda aka gani a jam’iyar PDP, da zarar APC ta hau mulki a 2015, “basu da juriyar su bada aiki su fara samun albarkaci cikin aikin, sai dai a nemi dala, a sa riba, a karya Naira. Abinda ya kawo mu halin da ake ciki ke nan har yau. Sai dai a ce, an sami korona, za a je a bada tallafi, a dauko Naira miliyan 10, nan kuwa ba a bada Naira miliyan 10 ba. Duk sauran an kame an je an sayi dala da su.” Ya ce, galibin wadanda ke gwamnatin talakawa ne wadanda kuma ke da talaucin zuci.

Dan takarar mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, mataki na biyu da zasu dauka na hana cin hanci da rashawa shine gudanar da gwamnatin da bata barna, ta wajen zama misali, da sa ido, da kuma tabbatar da aiwatar da dokokin da ke kasa na yaki da cin hanci da rashawa da yin hukumci-tabbatar da ganin doka ta yi halinta.

Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed
Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed

Tattalin Arziki

Saneta Datti ya bayyana cewa, idan jam’iyar Labor ta kafa mulki, daga ranar farko zata kafa waiji da zai hana Naira sake faduwa ta wajen toshe duk kafofin da suka haifar da wannan matsalar karkashin gwamnati mai ci yanzu. Bisa ga cewarshi, gwamnatin Labor zata haramta ba mukarraban gwamnati da iyalansu damar kane kane da damar samun dalar Amurka, ta kuma daidaita farashin dala ya zama daya ko biyu. Na uku kuma, gwamnati za ta yawaita samar da dalar yadda zata wadata ta daina hauhawa. Hakan zai sa wadanda suka tsorata, masu zuba jari zasu samu su shiga ciki.

Yace “idan gwamnatin ta dauki wadannan matakai aka samu aka koma noma, an koma kasuwanci, an rage ta’addi, an rage satar jama’a da garkuwa da makamantansu, ana tafiya ana walwala, tattalin arziki zai habaka. Jiragen sama zasu dawo suna aiki ‘yan kasuwa su yi cinikinsu suna samun riba.”

Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed
Yakin neman zaben Peter Obi da Yusuf Datti Baba Ahmed

Kwarin Guiwar Cin Zabe

Saneta Ahmed Datti ya bayyana cewa, jam’iyarsu tana da kwarin guiwa zata iya cin zabe kasancewa ‘yan Najeriya sun sallama jam’iyar APC sabili da aya da ta gasa masu a hannu. Yace a ko yaushe mutane suna tuna irin alkawuran da jam’iyar APC ta yi da bata cika ba. Bisa ga cewarshi, ‘yan Najeriya ba za su sake irin wadannan kura-kuran ba.

Ya bayyana cewa, ba a taba samun lokacin da mutum ya tsaya takara bisa cancanta ba kamar ‘yan takarar shugaban kasar da jam’iyar Labor ta tsayar. Yace duk da yake a addinance ba a gadara da ilimi, bisa ga kwarewar da suka samu sun san suna da cancanta. Yace Peter Obi yana fahariya da irin nasarorin da ya samarwa kanshi a matsayin dan adam wanda duk da ba dan siyasa ba ne, aka yi ta gwaggwarmaya da shi, da ya kai ga, saboda da shi aka canza tsarin zaben Najeriya domin jajircewarshi da neman ganin an yi adalci da ya yi ta kalulabantar zabensa da daka danne har kotun koli. Shi kuma a matsayin mai takarar mataimakinsa, ya yi fice a fannin ilimi da kishinsa na daukaka addinin Musulunci.

Bisa ga cewarshi, abinda ya banbanta jam’iyar Labor da sauran jam’iyu shine, sauran jam’iyun suna gadara da kudi ne da suka tara da ya yi masu yawa suke neman hanyar amfani da su su nemi mulki.

Wanene Yusuf Datti Baba Ahmed?

Saneta Yusuf Datti Baba Ahmed dan shekaru 53 da haihuwa Bazazzagi ne wanda aka haifa a Zariya. Kafin kafa jami’ar Baze a birnin tarayya Abuja, dan takarar mataimakin shugaban kasar ya yi siyasa a jam’iyu hudu idan aka hada da jam’iyar Labor, ya yi siyasa a jam’iyun CPC, PDP da ANPP kafin komawarsa jam’iyar Labor. Kafin nan ya yi wakilcin mazabarshi a majalisar wakilan tarayyar Najeriya inda ya kasance daya daga cikin wadanda suka jajirce suka hana Obasanjo tazarce, ya kuma wakilci kaduna a majalisar dattijai. Kafin Peter Obi ya zabe shi a matsayin abokin takararsa na shugabar kasa, Datti, ya nimi tsayawa takarar shugaban kasa da kuma gwamnan jihar Kaduna a lokuta dabam dabam sai dai bai kai ga nasara ba.

‘Takararmu A Jam’iyyar Labour Ta Na Firgita ‘Yan Adawa – Dr Datti Baba-Ahmed 
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:27 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG