Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda ISWAP Ta Kubutar Da Mutum Goma Daga Sansanin Boko Haram


Majiyoyi sun ce daga cikin mutanen da aka kubutar har da ma'aikatan agaji, wadanda kungiyar ta Boko Haram ta sace su a shekarar da ta gabata.

An saki mutane goma da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da su a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda wasu majiyoyin tsaro uku da wasu makusanta biyu na wadanda aka saka suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Majiyoyin sun ce mutanen, ciki har da ma'aikatan agaji, wadanda kungiyar ta Boko Haram ta sace su a cikin shekarar da ta gabata.

An sake su ne da misalin tsakar rana (1100 GMT) a ranar Litinin kuma aka kai su wani asibiti a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Bayanai sun ce kungiyar ISWAP mai ikirarin kafa daula a Afirka ta Yamma, wacce kishiya ce ga Boko Haram, ta saki mutanen bayan da ta same su a wani sansanin Boko Haram, amma har yanzu ba a san dalilin da ya sa suka sake su ba.

Karin bayani akan: Maiduguri, jihar Borno, ISWAP, UNHCR, Boko Haram, Majalisar Dinkin Duniya, Nigeria, da Najeriya.

Wani mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya bai bai ce komai ba a lokacin da aka nemi ya yi karin bayani kan lamarin.

Mai magana da yawun hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, Roland Schoenbauer ya tabbatar da cewa daya daga cikin ma’aikatansu, Idris Abubakar Garba, da aka sace a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a watan Janairu, na daya daga cikin wadanda aka sako.

-An hada wannan labarin daga rahotannin kamfanin dillancin labarai na Reuters

XS
SM
MD
LG