Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Marcelo Ya Yi Ban-Kwana Da Real Madrid Cikin Hawaye


Marcelo
Marcelo

“Ya zama dole na godewa Raul Gonzalez, wanda ke zaune a nan, ka taimaka min sosai a lokacin da na zo. Ba zan manta yadda ka ba mu kyauta ba da shawara, a lokacin da aka haifi dana Enzo. A ko da yaushe, da kai nake koyi.” In ji Marcelo.

Cikin yanayi na alhini, dan wasan baya na kungiyar Real Madrid Marcelo ya yi sallama da kungiyar a wani biki da aka shirya masa.

Marcelo ya bar Madrid ne bayan kwashe kakar wasanni 16 da kungiyar ta Sifaniya, lamarin da ya kai shi ga zubar da hawaye yayin da yake jawabi.

Dan wasan mai tsaron baya na gefen hagu, ya yi shiru yayin da yake magana akan Raul Gonzalez, daya daga cikin tsoffin ‘yan wasan kungiyar da suka halarci bikin a Madrid, inda ya sunkuyar da kai yana zubar da hawaye kamar yadda AP ya ruwaito.

“Ya zama dole na godewa Raul Gonzalez, wanda ke zaune a nan, ka taimaka min sosai a lokacin da na zo. Ba zan manta yadda ka ba mu kyauta ba da shawara a lokacin da aka haifi dana Enzo. A ko da yaushe, da kai nake koyi.” Marcelo dan asalin kasar Brazil ya ce.

Dan shekara 34, Marcelo ya kammala taka leda a kungiyar ta Real Madrid ne bayan da ya daga kofin Champions League a karo na biyar a watan da ya gabata.

Ya kuma taimakawa kungiyar ta lashe kofin gasar La Liga guda shida, kofin UEFA Super Cup guda uku, Copa del Reys biyu da kuma Spanish Super Cup biyar.

Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya bai wa Marcelo kyautar azurfa mai tambarin kungiyar yana mai cewa kofar kungiyar a bude take a ko da yaushe ga Marcelo.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG