Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Sojoji Suka Kashe '‘Yan ta’adda' Biyar A Kaduna – Gwamnati


Gwamna El Rufai (Facebook/El Rufai)
Gwamna El Rufai (Facebook/El Rufai)

Karamar hukumar Giwa na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar hare-haren 'yan fashin daji a jihar Kaduna.

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce dakarun kasar sun dakile wani hari da “’yan ta’adda” suka yi niyyar kai wa a Kwanar Bataro da ke karamar hukumar Giwa.

Hukumomin jihar sun an kuma kashe ‘yan ta’adda biyar.

Wata sanarwa da Kwamishinan tsaron cikin gida Samuel Aruwan ya fitar ta ce sojojin suna aikin sintiri ne a yankin na Giwa a lokacin da suka samu bayanan sirri da ke cewa ‘yan ta’addan sun nufi garin da ake kira Fatika.

“Hakan ya sa dakarun suka dunguma zuwa yankin Marke da Ruheya don kai dauki.”

“A lokacin da tsagerun suka hango dakarun, sai suka nemi tserewa. Amma sai sojojin suka yi musu kofar rago a yankin Kwanan Bataro inda aka yi musayar wuta, a sanadiyyar hakan biyar daga cikin ‘yan ta’addan suka mutu.” In ji Aruwan.

Sanarwar ta ce gwamna Malam Nasiru El Rufai ya yi matukar farin ciki da wannan nasara inda ya jinjinawa sojojin kasar kan matakin da suka dauka na gaggawa wajen kai dauki.

Yankin karamar hukumar na Giwa ya sha fama da matsalar hare-haren ‘yan fashin daji, wadanda a baya-bayan nan suka kashe mutum sama da 30 a harin da suka kai wasu kauyuka da ke yankin.

XS
SM
MD
LG