Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sake Tare Hanyar Kaduna-Zuwa Birnin Gwari, Sun Sace Mutane Da Dama


Makaman Da Yan Sanda Suka Kwace Daga Wasu Bata-Gari
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:12 0:00

Wasu makamai da 'yan sandan Najeriya suka kama.

A karo na uku a jere cikin wannan mako 'yan-bindiga sun sake tare hanyar Kaduna-zuwa Birnin Gwari inda su ka datse ayarin motoci masu rakiyar jami'an tsaro, su ka kashe mutane sannan su ka sace wasu da dama.

A ranar Talatar wannan makon ce dai 'yan-bindigan su ka tare ayarin motochin da ke kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna inda su ka kashe mutane biyu da jikkata mutane goma, sannan a ranar Laraba ma su ka kara datse ayarin inda su sa ce mutane da dama, sai kuma gashi sun kara tare hanyar a jiya Alhamis har ma sun kashe mutane su ka kuma sace mutane da dama.

Alh. Zubairu Abdurra'uf Idris shine Dan-masanin Birnin Gwari, ya kuma bayyana cewa al'umar yankin su na cikin wani hali.

Mai magana da yawun rundunar'yan-sandan jahar Kaduna, ASP Muhammed Jalige ya tabbar, ya ce

datse ayarin motochin da 'yan-bindigan su ka yi cikin kwanaki uku a jere dai, a Laraba ne kawai suka sha da kyar saboda misayar wuta da su ka yi da jami'an 'yan-sanda.

Maganar matsalar hare-haren 'yan-bindiga a wasu sassan jahar Kaduna dai sun yi kamari cikin wannan wata da mu ke ciki har ta kai ga gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufa'i ya gana da shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin neman mafita.

Yanzu dai hanyoyin fita ko shiga jahar Kaduna sun zama abun tsoro saboda hare-haren 'yan-bindiga domin kuwa ko bayan hanyoyin Kaduna-zuwa-Abuja da kuma Kaduna-zuwa-Birnin Gwarin da ake fargaba, ita ma hanyar Kaduna-zuwa-Zariya yanzu ba ta da tabbas saboda yadda 'yan-bindigan su ka fara tare ta.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00


XS
SM
MD
LG