Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Kashe Mutum 11 A Katsina


Daya daga cikin yankunan da aka kai harin a karamar hukumar Batsari a jihar Katsina

Lamarin ya faru ne a daren ranar Talata inda ‘yan bindigar dauke da muggan makamai suka far wa yankunan na Batsari suka rika bi gida-gida suna kai hari.

Mutane da dama ne suka rasa rayukansu bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai a yankunan karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina da ke yammacin arewacin Najeriya.

Wasu rahotanni sun ce mutum 7 ne suka mutum yayin da wasu ke cewa adadin ya kai mutum 13. Kazalika wasu da dama sun jikkata kamar yadda bayanai suka nuna.

Amma hukumomin tsaro sun ce mutum 11 aka kashe yayin da aka jikkata wasu 13 kamar yadda kakakin ‘yan sandan jihar SP Gambo ya sanarwa manema labarai.

Maharan sun far wa yankunan Katoge da ‘Yanturaku ne akan babura.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Talata inda ‘yan bindigar dauke da muggan makamai suka far wa yankunan na Batsari suka rika bi gida-gida suna kai hari.

Rahotanni sun ce maharan sun kuma kona gidaje ciki har da na gwamnati, da shaguna da motoci da dama.

‘Yan fashin dajin sun kwashe tsawon lokacin tun daga daren ranar ta Talata zuwa kusan wayewar garin Laraba suna ta’asa a yankunan kamar yadda shaidu suka ce.

Mafi yawan wadanda suka ji raunuka wadanda aka harba ne yayin da suke kokarin tserewa hare-haren a cewar rahotanni.

Rundunar ‘yan sanda jihar ta ce ta tura mataimakin kwamishinan ‘yan sanda zuwa yankin hade da karin jami’an tsaro a wani mataki na tsaurara matakan tsaro.

XS
SM
MD
LG