Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAMFARA: An Sako Mutum 100 Da Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su


Fararen hula dari, da wasu yan bindiga dauke da makamai suka sace a farkon watan Yunin da ya gabata a kauyen Manawa da ke arewa maso yammacin Najeriya, sun sake samun ‘yanci bayan da aka kwashe kwanaki 42 da yin garkuwar da su, in ji hukumomin jihar Zamfara a ranar Talata.

"A ranar 8 ga Yuni, 2021, 'yan bindiga suka mamaye kauyen Manawa suka yi awon gaba da mazauna kauye 100 da suka hada da mata wanda galibinsu mata matasane masu ‘yaya, da maza da kuma yara," a cewar sanarwar 'yan sandan jihar ta Zamfara.

"Wadanda abin ya rutsa da su da ke hannun maharan kimanin wata daya da rabi ke nan, an sako su ba tare da an biya su kudin fansa ba," in ji wannan sanarwar, wacce ba ta fayyace yadda sakin ya gudana ba.

Shekara da shekaru ke nan da Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ke fama da yawan ayyukan ‘yan bindiga wadanda ke kai hare-hare, sace-sace da ya hada da sacen mutanen kauye, satar dabbobinsu da kuma kona gidajensu.

A kwanan nan rundunar sojoji ta tura sabbin sojoji, wadanda suka hada da jiragen yaki, a yankin don kawo karshen tashin hankalin “'yan fashi," wadanda su ma aka sauya ayyukan su cikin' yan watannin nan zuwa yawan sace-sacen yara 'yan makaranta ko yara daga manyan makarantu don neman kudin fansa .

‘Yan fashin kan fake cikin dazuzzukan dajin Rugu, wanda ya ratsa jihohin Niger, Katsina, Kaduna da Zamfara.

Jami'an na jihar Zamfara ne suka tattauna a kan sakin yara maza 344 da yan bindigan suka sace daga makarantar kwana da ke makwabtaka da jihar ta Katsina.

Karin bayani akan: jihar Zamfara, ‘yan bindiga​, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Kowane sakin, hukumomi na musanta biyan kudin fansar ga‘yan bindigan. Koda shike, akwai shakku ga masana tsaro waɗanda ke fargaban cewa wannan zai haifar da ƙaruwar sace-sacen mutane a yankuna da ke fama da matsanancin talauci kuma da ƙarancin tsaro.

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda tsohon janar din soja ne da ya hau karagar mulki tun daga shekarar 2015, na fuskantar karin suka game da gazawarsa ta samar da tsaro a kasar da ta fi kowace yawan jama'a a Afirka.

XS
SM
MD
LG