Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakar Ta'addanci Sai An Cire Son Zuciya, Bangaranci Da Siyasa


Babu shakka idan mahukunta za su cire siyasa don kawo karshen matsalolin 'yan bindiga a Najeriya za a yi nasara.

Masu fashin baki a Najeriya na ci gaba da bayyana mabanbantan ra’ayoyi game da matakin yin sulhu da ‘yan bindiga, domin kawo zaman lafiya a kasar, a wannan lokacin sojojin kasar sun musunta cewa sun gaza a yakin da suke yi da ‘yan ta’adda.

Malam Nasiru Zaharaddin, tsohon shugaban kungiyar ‘yan jarida a Najeriya, kuma mai sharhi akan al'amuran yau da kullum, ya na ganin akwai sauran rina a kaba akan maganar sulhu.

"Sulhu da ake yi da mafarauta, ya na daukar salo na daban, idan aka lura a baya akan yi sulhu da su, su sako wadanda suka kama, amma daga baya su sake kama mutane. Wannan yana nuna cewar ba su shirya kawo karshen miyagun dabi'unsu ba."

Tunda abun ya kai haka, kamata yayi mahukunta su tashi tsaye wajen amfani da karfi, da samar da dokoki masu tsauri ga duk wanda aka samu da laifin aikata danyen aiki mai kama da satar mutum.

Idan aka duba abun da ke faruwa a kasashen da ake fama da yaki, akan yi amfani da tsarin a ciza kuma a hura, har sai an samu kamo bakin zaren, akasarin matsaloli da ake fuskanta a Najeriya yanzu, ana sa siyasa da hakan yake kai wa ba a iya cin ma matsaya akan matsaloli da dama.

Abu da ya kamata a maida hankali akai shi ne, mahukunta su cire siyasa a cikin batun da ya shafi fadan makiyaya da manoma, mutannen kudu da na arewa, ta haka ne kawai za a iya samun kawo karshen matsalar da ake fama da ita a kasar.

A na iya sauraron tattaunawar Baba Yakubu Makeri a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:07 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG