Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaki Da 'Yan Bindiga: An Rufe Sadarwa A Jihar Sokoto


Kamfanonin sadarwa
Kamfanonin sadarwa

Wata sanarwa da mai bai wa gwamna Tambuwal shawara kan lamurran watsa labarai Muhammad Bello ya fitar, ta ce sabuwar dokar rufe kafofin sadarwa da ta soma aiki a ranar Litinin, ta shafi kananan hukumomin mulki 14 na jihar.

A ci gaba da daukar matakan yaki da ‘yan bindiga a jihohin Arewa maso yammacin Najeriya, an rufe kafofin sadarwa a kananan hukumomin mulki 14 a jihar Sokoto.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin Najeriya ta ke ci gaba da fatattakar ‘yan ta da kayar bayan, musamman a jihar Zamfara da ke makwabtaka da Sokoto, da ma wasu sassan jihar ta Sokoto.

A wata tattaunawa da Muryar Amurka, gwamnan jihar Sokoton Aminu Waziri Tambuwal ya ce tun tuni ya kamata gwamnatin tarayya ta dauki wannan matakin kan ‘yan bindigar kuma bai daya, kamar yadda gwamnonin jihohin da lamarin ya shafa suka yi matsaya tun shekaru 3 da suka gabata.

Ya bayyana cewa duk da yake aikin da sojin suke yi a jihar Zamfara yana tasiri sosai, to amma rashin daukar mataki lokaci daya a jihohin, ya sa ‘yan bindigar sun soma kwarara a makwabtan jihohi.

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal

To sai dai ya ce sabuwar dokar rufe sadarwa, da dokokin da aka kakaba a can baya na rufe kasuwanni da wasu tituna, da kuma haramta sayar da man fetur a jarka da sauransu, zai baiwa sojoji damar ci gaba da kuma fadada ayukansu na fatattakar ‘yan ta’adda.

Wata sanarwa da mai bai wa gwamna Tambuwal shawara kan lamurran watsa labarai Muhammad Bello ya fitar, ta ce sabuwar dokar rufe kafofin sadarwa da ta soma aiki a ranar Litinin, ta shafi kananan hukumomin mulki 14 na jihar.

Sun kuwa hada da Gada, Goronyo, Gudu, Illela, Isa, Kebbe, Sabon Birni, Shagari, Rabah, Tambuwal, Tangaza, Tureta Wurno da Dange Shuni, wadanda su ne suka fi fama da ayukan ‘yan ta’adda a jihar.

XS
SM
MD
LG