Accessibility links

Takaddama ta Barke da Hukumar Yada Labaru a Nijar


Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou,

A jamhuriyar Nijar dazu ne Hukumar tace labaru ta kasar da ake kira CSC ta kira wani babban taro a kasar domin duba hanyar samarda wani kundi na bai daya mai kumshe da taswirar ayukkan kafafen yada labarun kasar

Taron ya samu halartar shuwagabannin kafafen yada labaru na rediyo da talabijin to amma sai dai bisaga dukkanin alamu wadanda a ke taron don su ba su gamsu da shi sabon kundin ba.

Burin da hukumar ta CSC take da shi akan wannan taro da ta shirya shine na kyautata tsarin tafiyar kafafen yada labaru masu zaman kansu da na gwamnati domin inganta jaddawalin shirye-shiryen kafafun yada labarun, tare da kyautata yadda kafafun yada labarun suke gudanar da ayyukansu a jamhuriyar Nijar a cikin tsanaki ba tare da tsangwama ba.

Taron na kwanaki uku da hukumar tace labaran ta shirya wa kafafen yada labaru masu zaman kansu da na gwamnati a jamhuriyar Nijar na da niyyar hada kan kafafun, ta rattaba hannu akan wani kundi guda daya mai taswirar yadda kafafun yada labarun zasu zartar da ayyukansu a Nijar.
XS
SM
MD
LG