Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Wata Kasuwa A Borno


Daya daga cikin 'yan banga da aka fi sani da "Civilian JTF" yana aiki a kauyen Mafoni Jihar Borno watan Agusta 2013.

'Yan bindigar da suka yi shigar 'yan kasuwa sun kai farmaki kan kasuwar kauyen Gajiram jiya alhamis, suka kashe mutane akalla 15

Wasu 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan kungiyar nan ce ta Boko Haram, sun yi shigar 'yan kasuwa, suka kai farmaki kan kasuwar Gajiram a arewa maso gabashin Najeriya, suka kashe mutane akalla 15.

Har ila yau, 'yan bindigar sun cinna wuta a sakatariyar karamar hukumar, da ofishin 'yan sanda da kuma wani asibitin dake garin na Gajiram, mai tazarar kilomita 75 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

An kai wannan harin tun ranar laraba, amma labarin bai fara fitowa ba sai jiya alhamis a saboda rashin hanyoyin sadarwa da ba a maido da su ba har yanzu a jihar ta Borno.

Wani mai sana'ar sayarda kayan marmari dangin lemo a garin na Gajiram, yace ya tsira da ransa ta hanyar buya cikin jeji. Yace watakila wannan farmakin ramuwar gayya ce a saboda kama 'ya'yan kungiyar Boko Haram da aka jami'an tsaro suka yi a garin, bayan da 'yan bangar nan da ake kira "Civilian JTF" suka zakulo su.

Yace, "ina jin an kawo mana wannan harin a saboda yadda 'yan bangarmu na Civilian-JTF suka samu nasarar dakile munanan ayyukan rashin imani na 'yan Boko Haram ta hanyar nuna su ga jami'an tsaro cikin 'yan kwanakin nan."

Wani jami'in gwamnati da ba ya son a fadi sunansa, yace atoni-janar na Jihar Borno, Kaka Shehu Lawan, da kwamishinan 'yan sandan Jihar Borno sun ziyarci garin na Gajiram domin yin ta'aziyya tare da ganin irin barnar da 'yan bindigar suka yi..

'Yan bangar nan da ake kira "Civilian JTF" sun taimaka sosai wajen dakile ayyukan 'yan Boko Haram ta hanyar farauto su da mika su ga hukumomin tsaro. Wannan namijin aikin da suke yi a cikin tsananin kasada, ya sa yanzu 'yan bindigar suka fara auna su a hare-haren da suke kaiwa. A ranar jumma'a makon jiya ma, 'yan Boko Haram din sun kashe 'yan banga 24 a kusa da garin Monguno.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG