Accessibility links

'Yan Boko Haram Sun Kashe 'Yan Banga 24 A Monguno


Wasu matasa da suka fusata dauke da adduna da wukake a Konduga, 13 Agusta, 2013

An kashe matasan a lokacin da suka yi kokarin kamo 'ya;yan kungiyar Boko Haram a garin Monguno

An kashe wasu matasa 'yan banga su 24 a yankin arewa maso gabashin Najeriya, a lokacin da wani yunkurin da suka yi na kamo 'yan kungiyar Boko Haram yayi tsami, bayan da 'yan bindigar suka yi musu kwanton bauna.

Daya daga cikin 'yan bangar da ba ya tare da wadanda suka yi kokarin kamo 'yan Boko haram din jiya jumma'a a garin Monguno, Masta Mohammed, yace an yi kwanton bauna aka far ma 'yan bangar kafin su kai ga sansanonin na 'yan Boko Haram.

Yace matasan, wadanda ake kira "Civilian JTF" su fiye da 100 sun shiga cikin wannan farmakin da yayi tsami a lokacin da 'yan Boko Haram suka tare su a bayangarin Monguno.

Wani jami'in rundunar tsaro ta JTF da ba ya so a ambaci sunansa, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa mutane 24 aka kashe a wannan farmakin.

Da alamun irin matakan da gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan take dauka su na nakkasa kungiyar Boko Haram, amma a can baya ma, an sha nakkasa kungiyar sai ta sake kunno mkai daga baya.

Matasa 'yan bangar, wadanda akasari adduna da wukake ne kawai makamansu, sun taimaka sosai wajen kamo daruruwan 'yan Boko Haram tare da mika su ga hukumomin tsaro.
XS
SM
MD
LG