Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan bindiga Sun Hallaka ‘Yan banga Da Dama A Jihar Neja


Gungumin ‘Yan Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:18 0:00

Gungumin ‘Yan Bindiga.

Bayanai dai sun nuna cewa jami’an tsaron ‘yan bangar sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suka tunkari ‘yan bingar a kokarinsu na kwato wasu shanu.

Rahotanni daga jihar Nejan Najeriya na nuna cewa ‘yan bindiga sun hallaka wasu jami’an tsaron ‘yan banga su kimanin 30 a lokacin wata arangama.

Bayanai dai sun nuna cewa jami’an tsaron ‘yan bangar sun gamu da ajalinsu ne alokacin da suka tunkari ‘yan bingar a kokarinsu na kwato wasu shanu da suka sata daga yankin karamar hukumar Magama a cewar daya daga cikin ‘yan bangar da ya tsallake rijiya da baya.

Shugaban karamar hukumar Magama Hon. Sifiyanu Ibeto, ya ce ya zuwa lokacin da aka tuntube shi akan batun aukuwar lamarin ba su kammala tattara gawarwakin ba.

Kawo lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin bayani daga rundunar ‘yan sandan jihar Nejan domin kuwa kokarin samun kakakin ‘yan sandan DSP Wasiu Abiodun ya ci tura.

Karin bayani akan: Salihu Tanko, jihar Neja, jihar Nejan, Nigeria, da Najeriya.

Sai dai gwamnatin jihar Nejan, ta tabbatar da aukuwar lamarin kamar yadda sakataren Gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim Matane ya shedawa manema labarai.

A halin da ake ciki dai daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko dake garin Tegina har yanzu suna daji a hannun ‘yan binbinga. Amma Gwamnatin jihar Nejan ta ce tana can tana kokarin kubutar da su.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00


Dubi ra’ayoyi (10)

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG