Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Babbar Kwalejin Sojojin Najeriya Ta NDA


Kwalejin Horar Da Jami'an Soji - NDA, Kaduna
Kwalejin Horar Da Jami'an Soji - NDA, Kaduna

‘Yan bindiga sun kai hari a kwalejin horar da jami’an soji ta Kaduna wato NDA, inda suka kashe jami’ai 2, suka kuma yi awon gaba da wani babban jami’in kwalejin.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan bindigar da suke da yawan gaske, sun kai farmaki a kwalejin da ke kan titin filin jirgin sama a Afaka da ke cikin karamar hukumar mulki ta Igabi ne da sanyin safiyar Talata.

Haka kuma sun bayyana cewa maharan suna sanye ne da kakin soji, inda suka sha karfin masu gadi, kana suka dumfari gidajen jami’ai da ke cikin kwalejin.

Ko baya ga jami’an da aka kashe da kuma wanda aka sace, wasu da dama kuma sun sami raunuka a harin, kuma yanzu haka suna samun kulawa a asibitin kwalejin ta NDA.

Babbar kwaleji ta horar da jami’an soji ta kaduna, tana dab da kwalejin nan ta horar da dabarun aikin gona ta gwamnatin tarayya, inda ‘yan bindiga suka kai hari a ranar 11 ga watan Maris, suka kuma sace dalibai 39.

To sai dai an sako daliban bayan sun kwashe tsawon kwanaki 50 a hannun ‘yan bindigar, biyo bayan shiga tsakani na tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, da malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gummi.

XS
SM
MD
LG