Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Don Kwato Wani Yanki a Ivory Coast


Wata kungiyar yan bindiga a Ivory Coast ta kaddamar da wani hari don kwato yankin birnin tsakiyar kasar na Bouake daga sojojin gwamnati bisa bukatar cika musu alkawarin karin kudi.

A kalla mutum daya ya mutu, kuma rahotanni sun ce sama da mutane 20 suka jikata biyo bayan yin watsi da kashedi da yan tawayen suka yi cewa, kowa ya zauna a cikin gidansa.


Har iyau babu wata sanarwa daga ma’aikatar sojin kasar a kan nasarar kwantar da wannan tarzoma. Wani soja da ya bijire yace sojojinsu ba zasu ajiye makami ba kuma suna jiran dakarun gwamnati.


Sojojin gwamnatin suk kwace Bouake birnin mafi girma na biyu a Ivory Coast a ranar Juma’a.


Galibin sojojin tsofaffin yan tawaye ne da aka dauka aikin soja bayan wata takaitacciyar tarzoma a cikin watan Janairu.


An yiwa yan tawayen alkawarin biyansu wasu kudade idan suka ajiye makamai, amma gwamnati ta kasa cika wannan alkawari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG