Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sojoji 24 da 'Yan Sanda 21 a Buni Yadi


Kimanin sojoji 24 da ‘yan sanda 21 ne suka rasa rayukansu, biyo bayan wani hari da ‘yan bindiga wadanda ake zaton ‘yan Boko Haram ne suka kai a garin Yadin Buni dake Jihar Yobe, daya daga cikin jihohin dake da dokar ta baci a arewa maso gabashin Najeriya.

Shaidu sun gayawa Muryar Amurka cewa an kai wannan hari ne Litinin dinnan, kuma ba’a san iya adadin fararen hula da ‘yan bindigan suka kashe ba.

Wani jami’in rundanar tsaro ta hadin gwiwa wato JTF wanda muka sakaye sunnanshi yace ‘yan bindigan sun tafi da motocin yakin sojojin da motoci masu yawa mallakar JTF. Daga cikin wadanda aka kashe harda hafsin ‘yan sandan dake kula da karamar hukumar Gujuba.

Karamar Hukumar Gujuba dake jihar Yobe, mai shedkwata a Buni Yadi ta samu kanta a tsakiyar tashe-tashen hankulan Boko Haram inda a baya-bayannan ‘yan bindigan sukayi wa dalibai yankan raguna a Kwalijin Gwamnati ta Buni Yadi, da Makarantar Noma ta Jihar Yobe.

A baya-bayannan, wasu direbobin motocin haya da Muryar Amurka yayi magana dasu sunce mayakan Boko Haram sun kashe musu ‘yan uwa biyu, akan titunan dake zuwa birnin Maiduguri, kuma sun kara da cewa wasu daga cikin ‘yan bindigan na boyewa cikin bishiyu, suna harbin jama’a a cikin motoci dake wucewa.
XS
SM
MD
LG