Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sace Mataimakin Ministan Ayyukan Kasar Afghanistan


Ahmed Shah Wahid
Ahmed Shah Wahid

Wasu da ake zaton 'yan Taliban ne sun sace mataimakin ministan ayyukan kasar Afghanistan a birnin Kabul babban birnin kasar

Wasu 'yan bindigar da ba a san ko su waye ba, sun sace mataimakin ministan ayyukan kasar Afghanistan a Kabul babban birnin kasar, wannan ne na baya-baya a jeri sace-sacen manyan mutane a kasar.

'Yan sanda sun ce jiya Talata da safe aka fitar da Ahmad Shah Wahid daga cikin motar sa da karfi lokacin da yake kan hanyar sa ta zuwa unguwar Khir Khana ta arewacin Kabul domin gudanar da wani aiki.

Babu bayani game da dalilin sace shi. Kuma babu mahalukin da ya dauki alhakin sace shi.

Haka kuma a jiya Talata ofishin shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai ya zargi sojojin Amurka da kashe fararen hula uku cikin harin da jirgin saman yaki ya kai lardin Khost a gabashin kasar.

Shugaban na kasar Afghanistan ya fitar da wata sanarwar da ta bayyana cewa harin ya sabawa yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka kulla sannan yayi tir da Allah waddai da shi.

Rundunar sojojin taron dangi da Amurka ke jagoranta ta ce ta na binciken al'amarin.

An kai harin ne a daidai lokacin da jami'ai ke kirga kuri'un zaben shugaban kasar Afghanistan da aka yi cikin kwanciyar hankali kadaran-kadahan.

Kuri'un farkon da aka kidaya sun nuna cewa tsohon ministan kudi Ashraf Ghani da dan jam'iyar adawa Abdullah Abdullah su ne a sahun gaba. A cikin watan gobe ake kyautata zaton samun cikakken sakamakon zaben.
XS
SM
MD
LG